Manyan Hare-Hare 8 da Sojoji Suka Kai Wa Farar Hula Ta Sama a Cikin Shekaru 6 a Najeriya

Manyan Hare-Hare 8 da Sojoji Suka Kai Wa Farar Hula Ta Sama a Cikin Shekaru 6 a Najeriya

  • Sojoji sun kai hare-hare akalla takwas kan fararen hula a Najeriya a cikin shekaru shida, inda abin ya fi shafar Arewacin kasar kawai
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an yi asarar daruruwan rayuka a ire-iren haren-haren kuskure da sojojin ke kai wa, da sunan yaki da 'yan ta'adda
  • Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu manyan hare-hare takwas da sojojin Najeriya suka kaddamar kan fararen hula a Arewacin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Harin bam kan masu maulidi a Tudun Biri da ke Kaduna a kwanan nan ya jefa ayar tambaya a zukatan 'yan Najeriya, har sai yaushe ne sojoji za su daina kai hari kan fararen hula?

Rahotanni na shekaru shida ya nuna yadda sojoji suka kai hare-hare kan farareren hula musamman a Arewacin Najeriya, inda aka yi asarar rayukan daruruwan mutane.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

Nigerian Air Force/Sojojin Najeriya/Arewa
Sojoji sun kai hare-hare akalla takwas kan fararen hula a Najeriya a cikin shekaru shida, inda abin ya fi shafar Arewaci. Hoto: Nigerian Air Force
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Tribuneonline, ya yi bayani kan hare-haren sojojin Najeriya da suka kai ta sama, wanda ya yi ajalin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rann, Jihar Borno | Watan Janairu, 2017

Akalla mutum 57 ne suka mutu a wani harin bam da jirgin yakin sojin sama ya saki kan sansanin 'yan gudun hijira da ke Raan, karamar hukumar Kala-Balge, jihar Borno.

Sojoji sun kai harin ne a watan Janairun shekarar 2017, inda akalla mutum 120 suka samu munanan raunuka.

Damboa, Jihar Borno | Watan Afrelu, 2020

Jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya saki bam a kauyen Sakotoku a karamar hukumar Damboa, inda ya kashe akalla mutum 17, musamman mata da kananan a watan Afrelu, 2020.

An ruwaito cewa Korongilum ne sojojin suka yi niyyar farmaka, wani kauye mai tazarar kilo mita 12, inda ake zargin 'yan Boko Haram sun yi sansani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya: "Kar ku kuskura ku kara jefa bam kan fararen hula"

Kauyen Buhari, jihar Yobe | Watan Satumba, 2021

Mutane da dama sun mutu a harin bam da sojoji suka kai ta sama a kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari, jihar Yobe, a ranar 28 ga watan Satumba, 2021.

Kasa da mako biyu, jirgin yakin sojin sama ya halaka masu kamun kifi 20 a Kwatar Daban Masara, inda sojojin suka yi zargin mayakan kungiyar ISWAP ne.

Shiroro, jihar Niger | Watan Afrelu, 2022

Akalla kananan yara shida aka kashe yayin da jirgin yakin sojin sama ya saki bam a wani gida da ke Kurebe, karamar hukumar Shiroro, jihar Niger a watan Afrelu, 2022.

Lamarin ya faru ne a ranar 13 ga wata, inda yara suke kan hanyar komawa gida daga wajen dibar ruwa, sojojin suka sakar masu bam, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Harin bam a Katsina | Watan Yuli, 2022

A watan Yuli, 2022 ne jirgin yakin sojin sama ya saki bam kan mutanen garin Kunkunna da ke Safana, inda sojoji su ka ce sun kai harin ne da tunanin 'yan bindiga ne.

Kara karanta wannan

"Mun fada mugun hannu": Sheikh Yabo ya caccaki gwamnatin Tinubu kan kisan masu maulidi a Kaduna

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Safana a majalisar dokokin jihar, Abdul Jalal Runka ya tabbatar da lamarin, inda ya ce mace daya ce ta mutu, sauran 14 na asibiti.

Jihar Zamfara | Watan Disamba, 2022

A watan Disamba 2020, wani harin soji a jihar Zamfara ya kashe fararen hula da dama a musayar wuta da sojoji suka yi da wasu da ba a san ko su waye ba a Dansadau da ke Maru.

Akalla lamarin ya shafi mutum 70, inda aka kashe maza da kananan yara, kamar yadda shugaban garin Mutunji, Umar ya sanar.

Harin Nasarawa-Benue | Watan Janairu, 2023

Wani hari da aka kai jihar Nasarawa a watan Janairun 2023 ya kashe makiyaya 27, wadanda ke dawowa daga kiwo a jihar Benue, bayan da gwamnatin jihar ta karbe shanunsu.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kai harin, wanda ake kyautata zaton jirgi maras matuki na rundunar sojin sama ne ya kaddamar da harin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Tudun Biri, jihar Kaduna | Watan Disamba, 2023

A ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba 2023, sojoji suka saki bam kan masu maulidi a garin Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, inda akalla mutum 100 suka mutu.

Wannan dai shi ne karo na biyu da rundunar soji ta kai hari a garuruwan fareren hula a Arewacin Najeria a wannan shekarar.

Rundunar sojin Najeriya ta dauki nauyin kai farmaki tare da ba da hakuri, inda ta yi ikirarin cewa kuskure ne aka samu, ta kai hari da zaton 'yan ta'adda ne suka yi sansani.

Yan Najeriya da dama na fatan gwamnati za ta yi bincike kan ire-iren wadannan hare-hare da sojoji ke kaiwa kan fareren hula da sunan yaki da 'yan ta'adda.

Tinubu ya gargadi sojoji kan kai wa fararen hula hari

A wani labarin, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gargadi sojojin kasar da harin Kaduna ya zama na karshe da za su yi kuskuren kai wa fararen hula a kasar.

Tinubu ya yi alhinin abin da ya faru da masu maulidi a Tudun Biri, jihar Kaduna, inda harin sojojin ya kashe sama da mutum 100, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel