Yadda Sufetan 'Dan Sanda da Matasa Suka Lakadawa Tsinannen Duka Ya Rasu a Jos

Yadda Sufetan 'Dan Sanda da Matasa Suka Lakadawa Tsinannen Duka Ya Rasu a Jos

  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta mai muƙamin sufeta da aka kai wa farmaki a Jos da ke jihar Plateau
  • Rahotanni sun ce an farmaki dan sandan ne mai suna Ikale Muhammed ne a ranar 1 ga Maris yayin da yake kokarin kama wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi
  • Wanda ake zargin ya tsere, amma daga baya ya dawo da ‘yan acaba suka kai wa ‘yan sanda hari inda Muhammed ya samu munanan raunuka
  • 'Yan sanda sun kai dauki, sun kwato babur a wurin da abin ya faru yayin da hukumomi ke bincike don cafke wadanda suka aikata danyen aikin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wani sufetan dan sanda da aka ji masa munanan raunuka bayan farmakin da matasa suka kai masa a Jos da ke jihar Plateau ya rasu.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta tsallaka, ta kai harin ramuwar gayya a Neja, ta kashe bayin Allah

Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar Ikale Mohammed a Jos ta Arewa a jihar a jiya Talata 4 ga watan Maris, 2025.

An hallaka dan sanda a jihar Plateau
'Dan sanda da ya hadu da fushin matasa a Jos ya rasa ransa. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Jami'in 'dan sanda ya mutu bayan harin matasa

Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa dan sandan, Ikale Muhammed, ya rasu da misalin karfe 5:30 na safe a ranar 4 ga Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rasu ne yana karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham yayin da aka ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa don bincike.

An kai masa farmaki ne a ranar 1 ga Maris, 2025, a shataletalen Polo lokacin da yake kokarin kama wani mutum da aka samu da miyagun kwayoyi tare da wani dan sanda.

Majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya tsere, ya bar wata jaka da kwayoyi masu hadari cikinta, ciki har da tabar wiwi inda ya shiga unguwar Jenta Adamu.

Bayan ɗan lokaci kaɗan, ana zargin wanda ake tuhuma ya dawo tare da wata ƙungiyar masu babura, waɗanda suka kai wa 'yan sanda hari yayin da suke jigilar miyagun ƙwayoyin da aka kwato.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Dan sanda ya mutu bayan harin matasa a Jos
Yan sanda sun tabbatar da mutuwar jami'insu bayan lakada masa duka. Hoto: Hoto: Caleb Muftwang.
Asali: Facebook

'Yan sanda sun kaddamar da bincike kan lamarin

Yayin harin, dan sanda ya gamu munanan raunuka inda aka kwashe shi zuwa asibiti domin samun kulawa, cewar TheCable.

Daga bisani, an karo jami'an tsaro wurin da lamarin ya faru inda aka yi nasarar samun babur kirar 'Boxer'.

Rundunar yan sanda a jihar Plateau ta tabbatar da fara bincike domin zakulo wadanda suka wannan mummunan aiki.

Har ila yau, rundunar ta bukaci al'umma su ci gaba da ba jami'anta bayanai domin tabbatar da bincike mai zurfi kan lamarin.

'Yadda bindigogi 3,000 suka bace' - yan sanda

Kun ji cewa Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana takaicin yadda bindigu akalla 3,907 suka yi layar zana daga karkashin kulawar jami'anta.

Wannan ya biyo bayan yadda majalisar kasar nan ta taso rundunar a gaba bisa makaman da har yanzu, ba a kai ga sanin inda suke ba.

Rundunar ta aika sako mai kunshe da gargadin gaggawa ga manyan ma'aikatanta dake rassanta a kasar nan da su shiga taitayinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng