Majalisa Ta Amince da Bukatar Tinubu, Ta Fadi Amfanin Kara Kasafin Kudi zuwa N54.2trn
- Majalisar Wakilai ta amince da shawarar shugaba Bola Tinubu na ƙara kasafin kuɗin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2
- Wannan ya biyo karin kudin shiga da aka samu daga hukumomin gwamnati da su ka hada da hukumar kwastam da ta tattara kudin haraji
- Kakakin Majalisar Wakilai na Mataimaki, Philip Agbese, ya ce majalisar ta na goyon bayan karin da Shugaban Ƙasa ya yi a kasafin 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta amince da shawarar Shugaba Bola Tinubu na ƙara kasafin kuɗin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.
Wannan mataki ya samo asali ne daga ƙarin kuɗin shiga da hukumomin gwamnati suka samar, ciki har da Naira tiriliyan 1.4 daga Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS).

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard News ta ruwaito cewa sauran kuɗaɗen da aka tara sun haɗa da Naira tiriliyan 1.2 daga Hukumar Kwastam ta Ƙasa, da kuma Naira tiriliyan 1.8 daga wasu hukumomin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin majalisa na goyon bayan Tinubu
Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin Majalisar Wakilai na Mataimaki, Hon. Philip Agbese, ya bayyana aniyar majalisar na taimakawa Shugaban Ƙasa wajen tabbatar da amfanin dimokuraɗiyya ga 'yan Najeriya.
Ya ce:
“Majalisar Wakilai tana maraba da shawarar Shugaban Ƙasa na sake duba kasafin kuɗin 2025 domin ƙara yawan kuɗaɗen zuwa Naira tiriliyan 54.2.
"Wannan mataki na da ƙwarin gwiwa, domin yana nuna jajircewar gwamnatin nan wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da inganta rayuwar 'yan Najeriya.”
Dalilin majalisa na amince wa da bukatar Tinubu
Hon. Agbese ya jaddada cewa mayar da hankali kan muhimman fannoni, musamman noma, zai taka rawa wajen tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan
'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu
“Yayin da muke nazarin cikakken bayanin wannan kasafi, muna farin ciki da yadda aka bai wa wasu muhimman fannoni muhimmanci, musamman noma. Tare da shigar da kuɗi cikin Bankin Noma, ana sa ran wannan shiri zai ƙarfafa manoma, inganta ci gaban karkara, da kuma tabbatar da wadatar abinci.”
Ya kuma tabbatar wa 'yan Najeriya cewa Majalisar Wakilai ta 10, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas, za ta tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin kuɗin 2025 bisa tsari mai nagarta.
Majalisa ta dauki mataki a kan zargin Tchiani
A wani labarin, mun ruwaito cewa Majalisar Dattawa ta fara bincike kan zargin da shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi cewa Najeriya tana haɗa kai da Faransa.
Tchiani ya bayyana cewa akwai shiri na musamman da ake yi a kusa da Sokoto, wanda zai zama sansanin horar da ‘yan ta’adda domin jawo rashin tsaro da tayar da hankula a kasarsa.
Majalisar Dattawa ta yanke shawarar tafi ziyara a jihohin Sokoto, Zamfara, da Kebbi domin tantance gaskiyar zargin, inda kwamitinta zai kawo rahoto a cikin makonni hudu nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng