'Diyar Ganduje Za Ta Samu Babban Mukamin Gwamnati, Majalisa Ta Aika Sunaye ga Tinubu

'Diyar Ganduje Za Ta Samu Babban Mukamin Gwamnati, Majalisa Ta Aika Sunaye ga Tinubu

  • Majalisa ta kawo shawarar nada mutum 11, ciki har da ‘ya’yan manya a matsayin daraktoci a hukumar raya Arewa maso Yamma
  • Ana so Asiya Ganduje ta samu mukamin daraktar cigaban Al’umma, yayin da ɗan Sanata Wamakko zai iya shugabantar sashen bincike
  • Sauran daraktocin da akawo kawo sun hada da Khalil Bako, Sanusi Bala Turaki a bangaren kudi, da Garba Aminu a sashen matasa da mata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar tarayya ta roki a nada mutum 11, ciki har da ‘ya’yan manyan ‘yan siyasa, a matsayin daraktoci a hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC).

Wannan na kunshe ne a wasikar da Rt. Hon. Tajudeen Abbas, shugaban majalisar wakilai, da Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, suka sanyawa hannu.

Majalisar tarayya ta nada 'ya'yan Ganduje da Wammako matsayin daraktocin hukumar NWDC.
Majalisa na so Tinubu ya amince da nadin 'yar Ganduje da dan Wammako matsayin daraktocin NWDC. Hoto: Dokin Karfe
Asali: Facebook

Majalisa ta roki a ba 'ya'yan Ganduje da Wamako mukami

Kara karanta wannan

"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa

A ranar Alhamis, jaridar SaharaReporters ta samu kwafin wasikar, wadda aka aike wa shugaban kasa Bola Tinubu domin amincewarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka nemi a nada akwai ‘yar shugaban APC kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma ɗan Sanata Aliyu Wamakko.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Sanata Aliyu Wamakko ya taba zama gwamnan jihar Sakkwato daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Mukamin da aka ba Asiya da dan Wammako

Majalisar na so Asiya Umar, diyar Abdullahi Ganduje, ta samu mukamin daraktar cigaban al’umma da karkara ta hukumar NWDC.

Haka kuma, an mika sunan Muhammad Mahdi Aliyu Wammako domin ba shi mukamin shugaban sashen shirye-shirye, bincike, kididdiga da bayanan gudanarwa.

Sauran wadanda ake so a nada sun hada da Khalil Bako a matsayin daraktan gudanarwa da albarkatun dan Adam, da Mustapha Ahmed Ibrahim, daraktan tsaro da muhalli.

Majalisa na neman amincewar Tinubu

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba sakataren APC a Kano Babban muƙami bayan minista ya bar kujerar

An kuma nemi Tinubu ya amince da nadin Sanusi Bala Turaki a matsayin daraktan kudi da kayayyaki; da Muhammed Kabir Sani a matsayin daraktan shari’a da hanyoyin doka.

Sauran da aka mika sunayensu su ne: Malik Anas a matsayin daraktan ma’adanai da aikin Noma; Alhasan Sidi Suleiman a matsayin daraktan cigaban masana’antu, da Garba Aminu, daraktan cigaban matasa da mata.

Wasikar ta ce:

“Ga sunayen waɗanda muke gabatar wa mai girma shugaban kasa domin amincewa da su a matsayin daraktoci na hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC)."

Tinubu ya nada 'yan majalisar gudanarwar NWDC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ƴan majalisar gudanarwa na hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC).

A watan Yulin 2024, shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa NWDC bayan majalisar tarayya ta amince da shi domin dawo da martabar yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.