Matakin da Majalisa Ta Dauka kan Zargin Janar Tchiani game da Lakurawa, Ta Na Kokwanto

Matakin da Majalisa Ta Dauka kan Zargin Janar Tchiani game da Lakurawa, Ta Na Kokwanto

  • Majalisar Dattawa za ta yi duba kan zargin da shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi kan game da Lakurawa
  • Majalisar za ta fara bincike kan zargin shugaban na cewa Najeriya tana haɗa kai da Faransa don haddasa rikici a kasar Nijar
  • Sanatoci za su kai ziyara jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi don tantance ko da gaske akwai ƙungiyar 'yan bindiga Lakurawa a yankunan nan
  • Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau ibrin , ya umurci kwamitoci su binciki lamarin kuma su bayar da rahoto a cikin makonni huɗu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta fara bincike kan zargin da Shugaban Ƙasar Nijar, Abdourahmane Tchiani game da Lakurawa.

Majalisar ta shirya binciken ne kan zargin cewa Najeriya tana haɗa kai da Faransa don haddasa rikici a Nijar ta hanyar ƙungiyar Lakurawa.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu

Majalisa ta shirya binciken zargin Janar Tchiani kan girke Lakurawa
Majalisar Dattawa za ta yi bincike kan zargin Janar Abdourahamane Tchiani game da Lakurawa. Hoto: The Nigeria Senate.
Asali: Facebook

Janar Tchiani ya zargi Najeriya da ta'addanci

Punch ta ce Majalisar Dattawa ta yanke shawarar kai ziyara don bincike a yankunan da aka ambata a cikin zargin musamman a jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan zargin shugaban Nijar cewa Najeriya tana da masaniya kan wanzuwar yan Lakurawa domin kawo mata cikas.

Hanar Tchiani ya ce:

"Akwai wani shiri da ake yi, amma shugabannin Najeriya sun san cewa akwai daji mai suna Gaba kusa da Sokoto.
"Ana so a mai da wannan daji sansanin horar da 'yan ta'adda Lakurawa."

Majalisar ta tabbatar da cewa ta dauki wannan ne domin tabbatar da akwai ko babu wannan ƙungiyar 'yan bindiga da ake kira Lakurawa, cewar Vanguard.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, APC, Kano wanda ya jagoranci zaman majalisar jiya, ya umurci kwamitocin Tsaro da su gudanar da cikakken bincike sannan su gabatar da rahoto a cikin makonni huɗu.

Kara karanta wannan

"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa

A yayin binciken, kwamitocin za su ba da shawarwari kan matakan diflomasiyya da tsaro domin dawo da kuma ƙarfafa dangantakar tarihi tsakanin Najeriya da Nijar.

Sanata ya musanta kasancewar Lakurawa a Najeriya

Kun ji cewa Sanata a jihar Kebbi, Adamu Aliero ya bayar da labari mai dadi kan ayyukan sojojin Najeriya wajen kakkabe Lakurawa da su ka kutso kasar.

Sanata Aliero, ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa an yi nasarar fatattakar yan taaddan daga Najeriya a yanzu babu labarinsu.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta bayar da karin kayan aiki ga dakarun sojojinta domin tabbatar da kawo karshen kungiyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.