Jami’a Ta Magantu a kan Zargin ‘Yan Majalisa Sun Nemi N480m daga Jami'o'i

Jami’a Ta Magantu a kan Zargin ‘Yan Majalisa Sun Nemi N480m daga Jami'o'i

  • Shugaban Jami’ar Tarayya, Gusau, Farfesa Muazu Abubakar, ya yi karin haske kan zargin da ake yi wa ‘yan majalisar dokoki na neman cin hanci daga jami’o’i
  • Bayaninsa na zuwa ne bayan wani rahoto ya zargi mambobin Kwamitin Ilimi na Jami’o’i na Majalisar Wakilai da neman Naira miliyan 480 daga jami'o'in tarayya
  • Jami’ar Tarayya, Gusau, ta bayyana cewa ba ta da masaniya a kan zargin an nemi kowace jami'a ta biya Naira miliyan takwas kafin a amince da kasafin kudinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Shugaban Jami’ar Tarayya, Gusau, Farfesa Muazu Abubakar, ya yi karin haske kan zargin da ake yi wa ‘yan majalisar dokoki na neman cin hanci daga jami’o’i.

Ya musanta zargin cewa mambobin Kwamitin Ilimi na Jami’o’i na Majalisar Wakilai sun bukaci Naira miliyan 480 domin amincewa da kasafin kudin jami’o’in tarayya na shekarar 2025.

Majalisa
Shugaban jami'ar tarayya ta Gusau ya yi karin bayani a kan zargin rashawa a majalisa Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 27 ga Janairu, wadda aka aikawa shugaban kwamitin, Abubakar Fulata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jami’ar ya karyata rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa ‘yan majalisa sun matsa wa shugabannin jami’o’i lamba domin biyan Naira miliyan 8 kowannensu don a amince da kasafinsu.

Shugaban Jami’a ya musanta zargin rashawa

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Shugaban Jami’ar Tarayya, Gusau, ya bayyana cewa rahoton ya ambaci wani “shugaban jami’a mai taurin kai” da ake zaton shi ne.

Ya ce tun farko bai yi niyyar mayar da martani ba, amma daga bisani ya yanke shawarar yin hakan domin karin haske a kan jita-jita da ka iya zama gaskiya a idanun jama’a.

A cewarsa:

“An ja hankalin Jami’ar Tarayya, Gusau, kan wani rahoto da ke yawo a yanar gizo mai taken Bincike: ‘Yan Majalisar Najeriya Sun Bukaci Naira Miliyan 480 daga Jami’o’i Domin Amincewa da Kasafin Kudi na 2025.

“Muna jaddada cewa babu wani daga cikin wakilan jami’a da suka halarci kare kasafin kudin da ya bayar da irin wannan bayani da ke yawo a kafafen yada labarai.
Muna kira gare ka, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai, da dukkan sauran mambobin kwamitin da su yi watsi da wannan rahoto na batanci da kuma son tada husuma, wanda manufarsa ita ce karkatar da hankalin jama’a da bata sunan jarida mai inganci.”

Shugaban Jami’a ya yaba wa Majalisa

Farfesa Muazu Abubakar ya jinjinawa kwamitin ilimi na majalisa bisa goyon bayan da ya bayar, inda ya bayyana zaman kare kasafin kudin a matsayin mai amfani, cike da fahimtar juna.

A jawabinsa, Kwamitin Ilimi na Jami’o’i na Majalisar Wakilai, Abubakar Fulata ya musanta wadannan zarge-zarge a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar.

Ya ce:

“Abin mamaki ne ga wani ya yi zargin cewa ‘yan majalisa sun bukaci ko da sisi daya a matsayin sharadin amincewa da kasafin kudi."

An zargi majalisa da neman rashawa

A baya, mun ruwaito cewa wani bincike da aka gudanar ya zargi wasu ‘yan majalisa ke amfani da matsayinsu wajen tilastawa shugabannin jami’o’i biyan cin hanci a shekarar 2025.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisar suna amfani da barazana da tsoratarwa wajen tilasta wa shugabannin jami’o’i su biya akalla Naira miliyan takwas kowannensu don amince wa da kasafin kudi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.