Gaskiya Ta Fito kan Rahoton Tura Bukatar Ƙirƙirar Jihohi 31, Majalisa Ta Fayyace Komai
- Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ba ta gabatar da kudirin kafa sababbin jihohi 31 ba, inda ta ce rahotannin da ke yawo kan hakan ba su da inganci
- Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu ya ce an karɓi ƙudirin kafa jihohi 31, ya ce wannan ƙudiri ba matsaya ba ce ta majalisar baki ɗaya
- Kudirin zai bi matakan doka, ciki har da taro na jin ra'ayi da amincewar rinjayen wakilan yankunan da ke neman a kafa sabuwar jiha a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta yi martani kan rahotanni da ke yawo game da ƙirƙirar sababbin jihohi a Najeriya.
Majalisar ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa tana neman kafa sababbin jihohi 31 da cewa ba su da inganci.

Asali: Facebook
An gabatar da bukatar ƙirƙirar sababbin jihohi

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi ya sanya wa hannu da aka wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman majalisar, Mataimakin Kakakinta, Hon. Benjamin Kalu ya bayyana cewa kwamitin sake duba kundin tsarin mulki ya karɓi ƙudirin kafa jihohi 31 daga ’yan majalisa.
“Kwamitin ya duba ƙudirin kafa sabbin jihohi bisa tanadin sashi na 8(1) na Kundin Tsarin Mulki na Najeriya, 1999, (da aka gyara).”
- Cewar sanarwar
Sabuwar jiha za ta samu ne idan kashi biyu bisa uku na wakilan yankin a Majalisar Dokoki da Majalisar Jiha suka amince da hakan.
Dangane da ƙudirin kafa sabbin ƙananan hukumomi, ya ce:
"Dole ne a gabatar da sakamakon kuri’a daga Majalisun jihohi zuwa Majalisar Tarayya.”
An umurci masu gabatar da ƙudiri su miƙa kwafinsa uku a dakin H331 na Majalisar Wakilai, Abuja, kafin Laraba, 5 ga watan Maris, 2025.
Matsayar Majalisar kan buƙatar kirkirar sababbin jihohi
Duk wasu kudiri na gyaran kundin tsarin mulki za su bi matakai da suka haɗa da taron jin ra’ayi da amincewa daga bangarori daban-daban.
Sanarwar ta ce saboda wasu sun gabatar da bukatar ƙirƙirar sababbin jihohi, hakan bai nuna ainihin matakin majalisar ne.
Majalisa ta tabbatar da cewa za ta yi aiki da doka kuma za ta tantance duk wasu kudiri bisa sharuddan da doka ta tanada.
Majalisar Wakilai ta nanata aniyar ta na gudanar da aikin sake duba kundin tsarin mulki bisa gaskiya da buƙatun al’umma.
Majalisa za ta binciki zargin Janar Tchiani
Kun ji cewa Majalisar Dattawa za ta yi duba kan zargin da shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi game da Lakurawa.
Majalisar za ta fara bincike kan zargin shugaban na cewa Najeriya tana haɗa kai da Faransa don haddasa rikici a kasar Nijar da ke makwabta.

Kara karanta wannan
An gabatar da bukatar kirkirar sababbin jihohi 31 a Najeriya, an jero su daga yankuna 6
Sanatoci za su kai ziyara jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi don tantance ko da gaske akwai ƙungiyar 'yan ta'addan na Lakurawa a yankunan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng