Bello Turji Ya Shirya Fito na Fito da Sojoji, Ya Kafa Sabon Sansani a Jihar Zamfara

Bello Turji Ya Shirya Fito na Fito da Sojoji, Ya Kafa Sabon Sansani a Jihar Zamfara

  • Awanni da kashe dansa, Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Dutsi da Yan Buki bayan tafka mummunar asara a hare-haren sojoji
  • Rahoto ya bayyana cewa Bello Turji ya mayar da sabon sansanin matsayin matattarar 'yan ta'adda da kula da wadanda aka raunata
  • Rundunar sojoji na ci gaba da samun nasarorin murkushe 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma a karkashin Operation Fansan Yanma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya kafa sabon sansani a dazuzzukan da ke tsananin Dutsi da Yan Buki, a gabashin Moriki.

Kafuwar sabon sansanin ta biyo bayan farmakin sojoji da ya yi sanadiyyar mummunan asara ga tawagar Bello Turji a Fakai da Shinkafi.

Rahoto ya yi bayanin yadda Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a Zamfara
"Yan kwanaki da kashe dansa, Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a Zamfara. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Facebook

Masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a cikin wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa Bello Turji ya kafa sabon sansanin domin hade kan ‘yan ta'addan da sojoji suka daidaita da kuma kula da lafiyar wadanda suka ji rauni.

Haka kuma, sabon sansanin zai zama wurin tsare wadanda aka sace daga hare-haren da Bello Turji ya kai garin Fakai, Kagara, da Maberaya.

An nemi mazauna Zamfara su ba da rahoto

Wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da suka tsira daga farmakin sojoji na neman mafaka a yankunan Gidan Jaja, Mayasa, da Kwashabawa.

An yi kira ga mazauna yankunan da su rika sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ‘yan bindigar ke yi.

Wannan na zuwa ne a yayin da sojojin Najeriya ke samun manyan nasarori a farmakin Operation Fansan Yanma.

Sojoji na samun nasara kan 'yan ta'adda

Rundunar sojoji ta Najeriya ta kara kaimi wajen gudanar da farmaki a karkashin Operation Fansan Yanma, inda suka lalata sansanonin ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

A cikin makon da ya gabata, sojoji sun kai farmaki kan sansanonin Bello Turji, suka kashe dimbin ‘yan bindiga tare da lalata wuraren buya.

Sojojin sun kuma kama wasu daga cikin ‘yan bindiga da masu tallafa musu da ransu, suna ci gaba da tabbatar da tsaron yankunan.

Duba wasu labarai kan Bello Turji a kasa

Bayan Kashe Dansa, Bello Turji Ya Shiryawa Sojoji Sabuwar Makarkashiya

Bello Turji Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ya Canja Salon Ta'addanci a Garuruwan Zamfara

Bello Turji Ya Fara Neman Agajin Yan Bindiga bayan Hare Haren Sojoji

Hare Haren Sojoji Sun Matsawa Turji, an Gano Shi da Zugar Mutane Yana Hijira

Bello Turji ya tsere da aka kashe dansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar tsaron Najeriya ta bayyana samun gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a Zamfara da kewaye, ciki har da kashe ɗan Bello Turji.

A farmakin na ranar 17 Janairu a Shinkafi, Kagara, Fakai, da Moriki, sojoji sun hallaka ɗan Turji tare da wasu mayakansa.

Manjo Janar Edward Buba ya ce an kashe ɗan Turji a tsaunin Fakai, inda aka gano sansanin ‘yan ta’addan, kuma Bello Turji ya tsere ya bar gawar dan nasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.