Sojoji Sun Illata Bello Turji Bayan Hallaka Ɗansa, an Jiyo Shi Yana Neman Agajin Yan Bindiga
- Rundunar 'Operation Fansan Yanma' ta kara kaimi a hare-harenta kan Bello Turji a Zamfara, ta lalata mafakan 'yan bindiga da ke Shinkafi
- Jiragen yakin sojojin sun kai farmaki inda suka lalata sansanonin 'yan bindiga, ciki har da makarantar da ake boye kayan abinci da makamai
- Sojoji sun kashe 'yan tawagar Turji da yawansu, ciki har da dansa, yayin da wasu daga cikinsu suka gudu zuwa Mangwarorin Gebe domin buya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Shinkafi, Zamfara - Rundunar sojoji ta ci gaba da kai farmaki mai tsanani kan shugaban yan bindiga, Bello Turji a jihar Zamfara.
Hare-haren sun kai ga lalata mafakan 'yan bindiga a Fakai a cikin karamar hukumar Shinkafi, inda Turji da tawagarsa suka dade suna boyewa.

Asali: Original
Yadda sojoji suka hallaka ɗan Bello Turji
Rahoton Zagazola Makama ya ce bayan samun nasarar hare-haren baya-bayan nan, an lalata sansanonin 'yan bindiga da ke karamar hukumar Sabon Birni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin inda aka kai hare-haren har da Zangon Dan Gwandi da Zangon Tsaika da Zangon Kagara.
Sojojin sun yi nasarar kona wata makaranta da ake amfani da ita wajen ajiye kayan abinci da makamai don hana Turji sake amfani da ita.
Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta tabbatar da cewa tawagar Turji ta yi asarar mutane da yawa ciki har da ɗansa.
An hallaka yaran Bello Turji a Zamfara
“Mun kashe dansa da wasu daga cikin jagororin tawagarsa."
"Mun kuma ji muryarsa cikin firgici yana neman agaji daga shugabannin 'yan bindiga guda bakwai, amma babu wanda ya zo."
- Cewar majiyar
A yayin hare-haren, an kashe wasu manyan tawagar Turji, yayin da wasu suka jikkata, cewar rahoton The Guardian.
Wasu daga cikinsu sun tsere zuwa Mangwarorin Gebe, inda ake zargin suna boye dabbobi da dukiyar sata.
Rundunar hadin guiwa sun farmaki yan bindiga
Hare-haren da aka gudanar sun samu jagorancin sojojin musamman tare da hadin gwiwar rundunar 'Operation Hadarin Daji' da kuma na rundunar sojojin ruwa SBS.
Wannan hari na musamman an yi shi ne don kawo karshen rashin tsaro da tarwatsa dukkan cibiyoyin 'yan bindiga.
Nasarar sojojin ta samo asali ne daga bayanan sirri da gargadi wanda ya taimaka wajen kwashe fararen hula daga wuraren da ake kai hare-hare.
Jiragen yakin Najeriya sun kai hare-haren sama kan miyagun wanda hakan ya rage karfin Turji.
Sojoji sun tare manyan hanyoyin tserewan Turji, inda rahotanni ke cewa an gan shi a Zangon Gebe, tare da tawagarsa dauke da makamai.
Bello Turji ya farmaki masallaci a Zamfara
A wani labarin, hatsabibin ‘yan ta’adda Bello Turji da mabiyansa sun farmaki masallacin Birnin Yaro a jihar Zamfara yayin da ake tsaka da sallah.

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin
Rahotanni sun tabbatar da cewa Turji ya sace adadi mai yawa na masu ibada, inda ya mika su cikin daji domin garkuwa da su.
Ana zaton Turji ya kai harin ne saboda rugugin wuta da ya ke sha daga Sojojin 'Operation fansan yamma' a kokarin kawo karshensa.
Asali: Legit.ng