Yadda Bello Turji Ya Tsere, Ya bar Sojoji Suka Kashe Dansa
- Sojojin Najeriya sun yi bayani bayan kashe ɗan ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji tare da wasu mayakansa yayin farmaki
- Dakarun soji sun lalata matattarar ‘yan ta’adda a yankin Fakai, Shinkafi da Kagara, tare da ceto mutane da aka yi garkuwa da su
- Manjo Janar Edward Buba ya bayyana Bello Turji a matsayin matsoraci bayan ya gudu ya bar ɗansa da mayakansa da sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta yi magana bayan samun gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a yankin Zamfara da kewaye.
A wani farmaki da aka gudanar ranar 17 ga Janairu, sojojin sun kashe ɗan Bello Turji, babban ɗan ta’adda da aka jima ana farautarsa.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ne ya yi magana bayan kai farmakin.

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashe dan Bello Turji da lalata sansanin Fakai
A yayin farmakin da aka gudanar a yankin Shinkafi, Kagara, Fakai, Moriki, Maiwa da Chindo, sojoji sun yi nasarar hallaka ɗan Bello Turji tare da wasu daga cikin mayakansa.
Daraktan watsa labaran rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an kashe ɗan Turji a wani tsauni da ke Fakai, inda aka gano sansanin ‘yan ta’adda.
“A wannan farmakin, sakin wutar sojoji ya haifar da mummunan hasara ga ‘yan ta’adda, inda aka lalata cibiyar samar da kayan aiki da suke amfani da ita,”
- Manjo Janar Edward Buba
Yadda Bello Turji ya tsere ya bar dansa
Bello Turji da ya shahara da tsokana da yin barazana ga jami’an tsaro, ya tsere daga sansaninsa yayin farmaki da aka kai masa ya bar ɗansa da sauran mayaka.
Rahotanni sun nuna cewa haka ya sanya Manjo Janar Edward Buba ya siffanta Bello Turji a matsayin matsoracin gaske.
A cikin nasarorin farmakin, sojoji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da suke tsare a hannun Turji da mayakansa.
Nasarar sojojin ta samu yabo daga jama’a, musamman mazauna yankunan da aka gudanar da farmakin.
Farmaki kan sansanin Idi Mallam
A wani farmaki daban, rundunar sojoji ta kai hari kan sansanin wani ɗan ta’adda, Idi Mallam, a dajin Zango-Kagara.
Sojojin sun kashe mutum uku daga cikin mayakansa tare da kama wasu mutum uku da ake zargin suna taimaka musu.
“A yayin farmakin, an kwato manyan bindigogi guda biyu, AK47 ɗaya tare da alburusai 11, da wasu dabbobi da aka sace, wadanda suka haɗa da shanu 61 da tumaki 44,”
- Manjo Janar Edward Buba
Jajircewar rundunar sojoji kan tsaro
Channels Television ta rahoto cewa Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa rundunar sojoji tana ci gaba da nuna ƙwazo wajen kawar da ta’addanci a Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan ‘yan kasa.
Kakakin rundunar ya kara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, sojoji za su ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda har sai an tabbatar da tsaron kasa baki ɗaya.
An gano gidan da ake kera makamai
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kai samame kan 'yan ta'adda a wasu jihohin Najeriya.
Legit ta wallafa cewa jami'an 'yan sanda sun gano wani gida da ake kera makamai ga 'yan ta'adda a jihar Benue tare da kama wasu mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng