Hare Haren Sojoji Sun Matsawa Turji, an Gano Shi da Zugar Mutane Yana Hijira

Hare Haren Sojoji Sun Matsawa Turji, an Gano Shi da Zugar Mutane Yana Hijira

  • An abbatar cewa jagoran 'yan bindiga, Bello Turji ya koma sabon mafaka a gabashin Dutsin Birnin Yaro domin tserewa tsauraran farmakin sojoji a Fakai
  • An tabbatar da cewa Turji ya sauya wurin ajiyar wadanda ya sace zuwa dazukan Dajin Jajjaye, Zaman Gira, Birnin Yaro, da Dogon Karfe
  • Sabbin 'yan bindiga sama da 100 sun raka wadanda aka sace, suna daukar matakan tsaro a hanyar Kwanar Jalop da ke tsakanin Jangeru da Birnin Yaro
  • Wannan na zuwa ne yayin da sojoji suka matsa wurin kai munanan hare-hare wanda ya jawo mummunan illa ga rikakken dan ta'addan, Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Hatsabibin dan ta'adda, Bello Turji yana ci gaba da shan matsin lamba daga hare-haren rundunar sojoji.

Yayin da sojoin ke tsaurara farmaki a yankin Fakai, Bello Turji ya dauke wadanda ya sace zuwa mafaka a gabashin Dutsin Birnin Yaro.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Bello Turji ya kwashe wadanda ya sace zuwa wasu dazuka
Hare-haren sojoji sun rikita Bello Turji yayin da ya fara neman mafita a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sojoji sun illata tasirin Bello Turji a Zamfara

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka inda ya ce dukkan alamu sun nuna Turji yana neman mafita ne a yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni sun tabbatar da rundunar sojoji ta ruguza wani ginin makaranta a kauyen Fakai a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

An tabbatar cewa an lalata ginin ne da ake amfani da shi wajen adana kayan abinci na shugaban ‘yan bindiga Bello Turji.

Ganin ya kasance ginshikin adana kayan abinci na 'yan bindiga, wanda ke da muhimmanci ga ayyukansu lamarin da ake ganin zai rage musu ƙarfi.

An gano Turji yana hijira zuwa wasu dazuka

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wadanda aka sace an tafi da su zuwa wurare da ke tsakanin dazukan Dajin Jajjaye, Zaman Gira, Birnin Yaro, da Dogon Karfe.

Wannan sauya wuraren ya kunshi gungun 'yan bindiga, wanda ake tunanin na daga cikin dabarun Turji ce don tserewa da ci gaba da tattaunawa kan kudin fansa.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Bayanai sun nuna cewa Turji ya tura sabbin gungun 'yan bindiga don tsaron wadanda aka sace da karbar kudin fansa.

Musabbabin daukar mataki da Turji ya yi

An gano cewa Turji ya dauki matakin ne da daren jiya Asabar, bayan sallar Isha, inda akalla 'yan bindiga 100 suka bar Fakai zuwa wani wuri kusa da Shinkafi.

Wasu na ganin akwai bukatar gaggawa na tura jami'an tsaro tsakanin Jangeru da Birnin Yaro, musamman a Kwanar Jalop.

Ana tunannin wannan ne kadai hanyar da 'yan bindigan ke amfani da ita domin tsira daga munanan hare-haren sojoji.

Sojoji sun yi nasarar kashe dan Bello Turji

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar 'Operation Fansan Yanma' ta kara kaimi a hare-harenta kan Bello Turji a Zamfara, ta lalata mafakan 'yan bindiga da ke Shinkafi.

Jiragen yakin sojojin sun kai farmaki inda suka lalata sansanonin 'yan bindiga, ciki har da makarantar da ake boye kayan abinci da makamai.

Sojoji sun kashe 'yan tawagar Turji da yawansu, ciki har da dansa, yayin da wasu daga cikinsu suka gudu zuwa Mangwarorin Gebe domin buya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.