Bello Turji Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ya Canja Salon Ta'addanci a Garuruwan Zamfara

Bello Turji Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ya Canja Salon Ta'addanci a Garuruwan Zamfara

  • Bello Turji ya yi barazana ga mazauna kauyukan kusa da Shinkafi, yana cewa zai kai hare-hare ga masu zuwa kasuwar Shinkafi
  • Ana ganin wannan barazana a matsayin kokarin Turji na ɓoye motsinsa da kuma gujewa ayyukan sojoji da ake gudanarwa a kansa
  • Jami'an tsaro suna ƙara kaimi domin kama Bello Turji, inda har aka rahoto cewa sojoji sun samu nasarar kashe dansa na cikinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Shugaban ƴan bindiga, Bello Turji ya yi barazana ga mazauna kauyukan kusa da Shinkafi, yana ikirarin kai hare-hare ga masu zuwa kasuwar garin.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa Turji ya gargadi mutanen da cewa duk wanda ya karya umurninsa, zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Bello Turji ya yi barazana ga mazauna Zamfara da sojoji suka tsananta hare-hare
Bello Turji ya fara neman hanyar tsira da sojoji suka zafafa hare-hare kansa. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Bello Turji ya yiwa Zamfarawa barazana

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa ana ganin wannan sabon al'amari a matsayin kokarin Bello Turji na guje wa jami'an tsaro da kuma ɓoye motsinsa.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Bello Turji yana son tabbatar da iko a yankunansa da kuma yin amfani da ra'ayoyin jama'a don sarrafa yadda ake kallonsa a wannan yanki.

Majiyoyi daga yankin Shinkafi sun shaida cewa babu wani rauni da aka ji wa Bello Turji sabanin wasu rahotanni da aka yada a baya.

Bello Turji na cikin tashin hankali

Duk da wannan, shugaban 'yan ta'addan yana ci gaba da boye motsinsa, kuma ana ganin yana wasan 'yar buya da jami'an tsaron gwamnati.

Majiyoyi sun bayyana cewa an ga Bello Turji a wasu kauyuka na kusa a jiya, inda aka ganshi a cikin damuwa da matsin lamba daga sojoji.

Ci gaba da kai hare-hare a kokarin kama Turji da rushe ƙungiyarsa ya haifar da rashin kwanciyar hankali a jihar Zamfara da kewaye.

Sojoji sun matsawa Bello Turji lamba

Jami'an tsaro sun ƙara zage dantse wajen gudanar da ayyukansu, inda aka yi kira ga mazauna yankunan da Turji yake da su ci gaba da sa ido da kai rahoton motsinsa.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya sake sauya mafaka, an gano shi da wasu rikakkun yan ta'adda 2, ya nadi bidiyo

An ce sojoji sun kara kaimin hare-hare ne a wani yunkuri na kawo karshen Bello Turji da sauran 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma.

Kamar yadda ake ci gaba da kokarin kama shi, Bello Turji a hannu daya na ci gaba da wasar 'yar buya da jami'an tsaro da kuma canja salon ta'addancinsa.

Zamfara: Sojoji sun kashe dan Bello Turji

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun zafafahare-harenta kan Bello Turji a Zamfara, ta lalata sansanonin ƴan bindiga a Shinkafi.

Jiragen yakin sojoji sun kai farmaki, inda suka lalata wuraren boye kayan abinci da makamai da ƴan bindiga ke amfani da su.

Sojoji sun kashe wasu daga cikin tawagar Turji, har da dansa, yayin da wasu ƴan bindiga suka tsere zuwa Mangwarorin Gebe domin buya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.