Bayan Kashe Dansa, Bello Turji Ya Shiryawa Sojoji Sabuwar Makarkashiya

Bayan Kashe Dansa, Bello Turji Ya Shiryawa Sojoji Sabuwar Makarkashiya

  • Hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, sake shirya mugun nufi ga dakarun sojojin Najeriya masu aiki a ƙarkashin rundunar Operation Fansan Yamma
  • Bello Turji ya umarci mayaƙansa da su yi wa dakarun sojojin kwanton ɓauna a yankin Issah na jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Umarnin yi wa dakarun sojojin kwanton ɓauna na zuwa ne bayan sun taso shi a gaba wajen farautarsa tare da sauran tsagerun da ke cikin ƙungiyarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Tantirin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga wajen dakarun sojojin Najeriya.

Majiyoyin sirri sun bayyana cewa Bello Turji ya umarci mayaƙansa da su yi kwanton ɓauna ga dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma.

Bello Turji zai farmaki sojoji
Bello Turji ya umarci a yi wa sojoji kwanton bauna Hoto: @bulamabukarti
Asali: Twitter

Bello Turji ya sa a yi wa sojoji kwanton ɓauna

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta sake taso Bello Turji a gaba, ta fadi abin kunyar da ya yi

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya tabbatar da hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi, 18 ga watan Janairun 2026.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya umarci mayaƙan na sa ne da su yi wa dakarun sojojin kwanton ɓaunan ne a yankin Issah na jihar Sokoto.

"Turji ya shahara wajen amfani da dabarun yaƙin sunƙuru, kuma wannan umarnin kai harin yana daga cikin ƙoƙarinsa na kawo cikas ga ayyukan da sojoji suke yi don kawo ƙarshensa da ƴan ƙungiyarsa."

- Wata majiya

A sakamakon wannan bayani, an shawarci jami’an tsaro da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, musamman a manyan hanyoyin da za a iya kawo musu farmakin bazata.

Sojoji na farautar Bello Turji

A cikin ƴan kwanakin dai dakarun sojoji sun matsa lamba ga shugaban ƴan bindigan inda suke kai masa hare-hare babu ƙaƙƙautawa domin ganin bayansa.

Harin baya-bayan na da sojoji suka kaiwa Bello Turji ya yi sanadiyyar hallaka ɗansa tare da lalata wurin ajiye makamansa.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro ya fadi shirin Bello Turji bayan sojoji sun matsa masa lamba

Nasarar da jami'an tsaron suke samu a kan shugaban ƴan bindiga na nuna alamun cewa ƙarshen ta'addanci ya kusa zuwa.

Bello Turji dai ya daɗe yana ta'addanci a yankunan jihohin Zamfara da Sokoto inda ya yi sanadiyyar tayar da hankulan mutanen da ke rayuwa a wuraren.

Karanta wasu labaran kan Bello Turji

Bello Turji ya yi barazana ga mutanen Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, ya aika da.saƙon gargaɗi da barazana ga mutanen ƙauyukan da ke kusa da Shinkafi a jihar Zamfara.

Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare ga duk mutanen ƙauyukan waɗanda suke zuwa kasuwar Shinkafi domin gudanar da harkokinsu.

Kara karanta wannan

Oshiomhole ya cire tsoro, ya faɗi manyan ƙasa masu hannu a haƙar ma'adanai na haram

Mazauna yankin sun bayyana cewa ya yi gargaɗi kan cewa wanda ya sa ƙafa ya yi watsi da umarninsa, zai fuskanci hukunci mai tsananin gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng