An Karrama Sojoji 8 da Suka Ƙi Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 1.5 Daga Hannun Ɓarayin Shanu

An Karrama Sojoji 8 da Suka Ƙi Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 1.5 Daga Hannun Ɓarayin Shanu

  • Rundunar soji ta karrama wasu dakarunta guda takwas da ke a OPSH na hudu saboda sun ƙi karbar ci hancin naira miliyan 1.5 a Plateau
  • Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta ce wasu ɓarayin shanu ne suka ba dakarun cin hanci bayan da aka kama su
  • Kwamandan rundunar OPSH, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar wanda ya karrama dakarun ya yaba da rikon gaskiyar su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Plateau - Dakarun atisayen Safe Haven (OPSH) da ke aiki a jihar Plateau da wasu sassan jihohin Arewa, sun ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a Filato.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba MTN, Airtel da Glo umarnin abin da za su yi da layukan da ba su da NIN

Jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin James Oya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Jos.

Operation Safe Haven (OPSH)
Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun ƙi karbar cin hanci na N1.5m daga hannun ɓarayin shanu a Plateau. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Oya ya ce, sojojin da ke aiki a sashinsu na hudu, sun kama mutanen da ake zargin barayin shanu ne guda biyu wadanda suka ba su cin hancin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa jami'an takwas da suka ki karbar cin hancin ba kawai yabo kadai suka samu ba, har ma da tukuici daga kwamandan rundunar, Manjo-Janar Abdusalam Abubakar.

Abin da sanarwar ta kunsa

“Jami'an takwas da aka tura sashin OPSH na hudu, sun kama shanu 30 na sata a wani shingen bincike da ke kusa da Bisichi a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar.
“Wadanda ake zargin, Anas Usman da Gyang Cholly nan take suka tunkari jami'an da nufin ba su cin hanci don su barsu su tafi da shanun da suka sato."

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

- A cewar sanarwar.

Oya ya ce kwamandan wanda ya yabawa sojojin bisa wannan jarumtaka, ya bukaci sauran jami’an tsaro da su yi koyi da hakan a wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihar.

Karanta sanarwar a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel