Nasara: Sojojin Najeriya Sun Yi Luguden Wuta Kan Ƴan Ta'adda, Sun Tura da Dama Lahira

Nasara: Sojojin Najeriya Sun Yi Luguden Wuta Kan Ƴan Ta'adda, Sun Tura da Dama Lahira

  • Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram/ISWAP uku a yankin tafkin Chadi
  • Sojojin sun kuma kwato muggan makamai da kayan aikin ƴan ta'addan a samamen da ya ƙara nakasa su ranar Laraba
  • Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ce ta tabbatar haka a wata sanarwa, tana mai cewa bisa tilas ƴan ta'addan suka yi takansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram/Islamic State West Africa (ISWAP) uku a yankin tafkin Chadi.

Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Jumu'a, 29 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya jero jihohin Arewa 3 da ya kamata sojoji su tashi tsaye kan ƴan Bindiga

Sojojin Najeriya sun yi galaba kan yan ta'adda.
Sojoji Sun Ci Karfin Yan Ta'addan ISWAP, sun halaka mayaka 3 a tafkin Chadi Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A sanarwan kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce dakarun tare da haɗin guiwar jami'ar JTF sun yi nasarar tarwatsa sansanin da ƴan ta'adda ke taƙama da shi a Tinbuktu Triangle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami'an tsaron sun kai samame maɓoyar ƴan ta'addan ranar Laraba kuma yayin kazamin artabun da suka yi, ƴan ta'adda 3 suka baƙunci lahira.

Wasu daga cikin makaman da aka ƙwato

Sun kuma kwato wata motar yaƙi ƙirar MRAP, motar da ke ɗauke da bindigar kakkaɓo jiragen sama, bindigu da kuma harsasai.

Kakakin rundunar ya ce maharan sun farmaki sojoji ne da wata motar bama-bamai (VBIED), turmi, manyan motocin yaƙi, da kuma babura.

Ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun ji karfin luguden wuta na sojoji, lamarin da ya tilasta musu barin sansaninsu, makamai da kayan aikinsu, suka arce domin tsira.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Ya kara da cewa farmakin ya zama babban koma-baya ga ‘yan ta’addan, yayin da dakarun sojojin suka tura uku daga cikinsu zuwa lahira.

Sanarwan ta ce:

"Kayayyakin da aka kwato sun hada da MRAP daya, babbar motar yaƙi, bindigar Dushka daya, bindiga kirar AK 47 daya, da kuma bindiga kirar gida guda daya."

Wasu daga cikin nasarorin sojoji a wata ɗaya

A wani rahoton kuma Sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda sama da 900, sun kana wasu 621 a sassa daban-daban na kasar nan a watan Fabrairu.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ce ta bayyana haka yayin da take zayyana nasarorin rundunar soji a tsawon wata ɗaya ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel