Fargaba Da Zullumi Yayin Da Ɗaruruwan Yan Ta'addan Zamfara Suka Yi Hijira Zuwa Katsina

Fargaba Da Zullumi Yayin Da Ɗaruruwan Yan Ta'addan Zamfara Suka Yi Hijira Zuwa Katsina

  • Hankulan mutane a wasu kauyukan jihar Katsina ya tashi saboda isowar daruruwan yan ta'adda da suka yi hijira daga Zamfara, wasu mutanen sun fara barin gidajensu
  • Majiyoyi daga wasu kauyuka a karamar hukumar Safana da Batsari sun yi zargin hatsabibin dan bindiga, Dan-Karami ne ya taho da tawagarsa ya hade da takwararsa, Dan Modi-Modi
  • Wani shugaban al'umma wanda ya tabbatar da isowar yan ta'addan ya yi kira ga sojoji da Gwamnatin Katsina su yi kawo wa mutane dauki cikin gaggawa

Jihar Katsina - Daruruwan yan ta'adda karkashin jagorancin hatsabibin dan ta'adda, Dan-Karami, sun baro yankunan Zamfara sun dawo kusa da kananan hukumomin Safana da Batsari a Katsina.

Mazauna kauyukan sun ce yan ta'addan na tserewa ne daga luguden wuta da sojoji ke musu a Zamfara.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara a Arewa: An Kashe Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Addabi Al'umma

Taswirar Katsina
Mazauna kauyukan Katsina sun ce sun ga daruruwan yan ta'adda kan babura suna shigowa garinsu. Hoto: The Punch
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa sun yada zango a garuruwan Tsaskiya, Runka, Gora, Labo da wasu garuruwan a kananan hukumomin.

Mazauna kauyukan sun ce yan ta'addan sun hada kai da wani kasurgumin dan bindiga, Usman Modi-Modi, wanda ke adabarsu.

Mazauna kauyuka sun tabbatar da isowar yan ta'addan Katsina

Mutanen kauyen sun ce yan ta'addan sun taho yankin da shanu masu yawa.

Wata kwakwarar majiya ta fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, cewa:

"Kimanin yan ta'adan dubu da suka taho kan babura 300 sun kwana a daren ranar Asabar a kauyen Labo."

Ya kara da cewa yan ta'addan sun bazu a kauyuka a kalla biyar da ke iyaka da dajin Rugu da ke tsakanin Safana da Batsari da Zamfara.

Majiyar, amma, ta ce ba a tabbatar ko za su kafa sansani bane a nan ko kuma suna kan hanya ne.

Kara karanta wannan

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Mutanen kauyukan sunyi kira ga sojoji da Gwamnatin Jihar Katsina su dauki mataki cikin gaggawa kada su ba wa yan ta'adan daman fara kai hare-hare.

Dan-Karami da tawagarsa sun yi kaurin suna saboda kai hare-hare a kauyuka da birane a Zamfara da kai wa jami'an tsaro hari.

Shugaban al'umma ya yi martani

Wani shugaban al'umma da ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wa NAN cewa wasu yan kauyen sun fara kaura saboda gujewa fitina da ka iya tasowa.

Ya yi kira ga sojoji su turo jami'ansu su fatattaki yan ta'addan kafin su samu gindin zama.

Ya kara da cewa:

"Idan ba a dauki mataki yanzu ba, wannan yan ta'addan za su zama babban barazanar tsaro ga kananan hukumomi da dama, har da babban birnin jiha.
"Suna da yawa kuma suna da makamai. Gwamnati ta mayar da martani mai karfi domin kare mutane."

Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Kara Yin Muhimman Nade-Nade Saura Kwana 24 Ya Sauka Mulki

Akwai hatsabiban yan ta'adda da suka zama matsala ga al'ummar Najeriya a lokuta daban-daban.

Mafi yawancinsu sun hada laifuka da dama suna yi kamar kisa, garkuwa da mutane, fashi da makami, kai hare-hare da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel