Sojoji Sun Ragargaji Ƴan Ta'adda a Katsina, Sun Halaka da Dama

Sojoji Sun Ragargaji Ƴan Ta'adda a Katsina, Sun Halaka da Dama

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda masu tarin yawa a ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina
  • Sojojin na sama da ƙasa sun kuma samu nasarar lalata maɓoyar ƴan ta'addan wacce ke a tsaunin Tora
  • Jiragen sama ne dai suka fara kai wa ƴan ta'addan hari sannan sai sojojin ƙasa suka ƙarasa kakkaɓe ƴan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ɓangaren sama na rundunar Operation Hadarin Daji da Bataliya ta 17 ta rundunar sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda da dama a harin bama-bamai ta kasa da ta sama a jihar Katsina.

Sojojin sun kuma lalata maboyar ƴan ta’addan a wani samame a ranar 30 ga watan Janairu a tsaunin Tora, ƙaramar hukumar Safana ta jihar, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar galaba kan 'yan bindiga a jihar Arewa

Dakarun sojoji sun halaka yan ta'adda
Sojoji sun halaka yan ta'adda masu yawa a Katsina Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), Air Vice Marshall Edward Gabkwet, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, rahoton Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai harin a kan ƴan ta'addan

Gabkwet ya ce, jirgin saman NAF ne ya fara far wa wurin, inda daga nan ne sojojin ƙasa suka yi nasarar kakkaɓe ƴan ta'addan.

A kalamansa:

"Hotunan tantance ɓarnar da aka yi a yaƙin da kuma wasu bayanai da aka samu daga wasu majiyoyi sun nuna cewa harin da aka kai ta sama ya yi matuƙar rage ƙarfin ƴan ta’addan wanda daga nan ne sojojin ƙasa suka kai samame ba tare da ɓata lokaci ba.
"Hare-haren na haɗin gwiwa ya kai ga kashe ƴan ta’adda da dama tare da lalata maɓoyarsu a kan tudu, sun kuma ba sojojin ƙasa damar hawa tsaunin Tsora, wanda ya kasance maɓoyar ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Safana."

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da 'mata 55' ƴan rakon amarya ɗaki a jihar Arewa

Legit Hausa ta samu jin ta bakin Muhammad Garba, wani mazaunin jihar Katsina, wanda ya nuna jin daɗinsa kan wannan nasarar da sojojin suka samu.

Ya bayyana cewa nasarar abun a yaba inda ya yi addu'ar Allah ya ba su ƙarfin gwiwar ci gaba da ƙoƙarin da suke na kakkaɓe ƴan bindiga a jihar.

Ya yi nuni da cewa ana samun ci gaba sosai a fannin tsaro a jihar ta Katsina.

Sojoji Sun Sheƙe Ƴan Ta'adda Masu Yawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 185 a cikin mako ɗaya.

Sojojin sun kuma yi nasarar cafke miyagu 212 tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel