Dandutse: Ƴan Bindiga Sun Kashe Babban Soja da Wasu Jami'ai Biyu, Sun Tafka Ɓarna Kan Bayin Allah

Dandutse: Ƴan Bindiga Sun Kashe Babban Soja da Wasu Jami'ai Biyu, Sun Tafka Ɓarna Kan Bayin Allah

  • Sanatan shiyyar Funtua a jihar Katsina ya faɗi yadda ƴan bindiga suka kashe kaftin na gidan soja da wasu sojoji biyu a mazaɓarsa
  • Muntari Ɗandutse ya yi jawabi ne a zauren majalisar dattawa yayin gabatar da kudirin kashin kansa da ya shafi mazaɓarsa ranar Talata
  • Bayan haka ne majalisar dattawa ta yi shiru na minti ɗaya domin girmama waɗanda aka kashe a hare-haren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kashe babban jami'in soja da ya kai matsayin kaftin da wasu sojoji biyu a yankin Sabo, shiyyar Funtua a jihar Katsina.

Sanata mai wakiltar Katsina ta kudu (Funtua Zone), Muntari Ɗandutse ne ya bayyana haka, ya ce ƴan ta'addan sun aikata wannan ɗanyen aikin ne ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Sanata Muntari Ɗandutse.
Yan Bindiga Sun Kashe Kaftin da Sojoji Biyu a Katsina, Sanata Dandutse Hoto: Dandutse Support Group
Asali: Facebook

Ya yi magana ne a zauren majalisar dattawa a ranar Talata bayan gabatar da wani kudiri na ƙashin kansa da ya shafi al'ummar da yake wakilta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandutse ya bayyana cewa ko a ranar 21 ga watan Fabrairu, sai da ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 16 a yankin, kamar yadda The Cable ta tattaro.

Sanatan ya buƙaci jami'an tsaro su farka daga bacci

Ya kuma ƙara da yin kira ga hukumomin tsaro su kara zage dantse domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar mazaɓarsa ta Katsina ta kudu.

Ya ce:

"Ya kamata hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyi. ‘Yan bindiga sun kashe wani kaftin na soja da jami’ai biyu ranar Alhamis a Sabo."

Sanatan Muntari Dandutse ya koka da cewa ƴan bindiga na kai hare-haren kan al'umma duk da akwai tuƙin jami’an tsaro a garuruwan.

Kara karanta wannan

"A shigo da abinci" TUC ta gano hanya 1 da zata share hawayen talakawa, ta aike da saƙo ga Tinubu

Ya ci gaba da cewa:

"Wadannan al’amura marasa dadi suna faruwa ne lokaci bayan lokaci duk da akwai jami’an tsaro da ke zaune a yankuna.
"Idan ba a dauki matakan gaggawa na tunkarar kalubalen tsaron nan ba, jama'ar wannan yanki masu ƙaunar zaman lafiya ba za su iya gudanar da ayyukan su na noma ba."

Wane mataki majalisa ta ɗauka?

Bayan haka, majalisar dattijai ta yi shiru na minti daya domin girmama wadanda aka kashe a hare-haren.

Ta kuma bukaci hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ta samar da kayan agaji ga duk wadanda hare-haren ya shafa.

An ceto mutum 40 daga hannun ƴan bindiga

A wani rahoton kuma Yan sanda da taimakon mafarauta sun yi nasarar halaka ƴan bindiga masu yawa tare da ceto mutane 40 da aka yi garkuwa da su a Taraba.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP David Iloyanomon, ya ce jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga, sun kamo 10 daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel