Yan Sandan Saurauniya Na Bata Sunan Yan Sanda, PSC Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka a Kansu

Yan Sandan Saurauniya Na Bata Sunan Yan Sanda, PSC Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka a Kansu

  • Hukumar 'yan sanda (PSC) ta fara wata tattaunawa da babban sufetan rundunar 'yan sanda don rushe sashen 'yan sandan sarauniya na rundunar
  • A cewar shugaban hukumar, Solomon Arase, korafe-korafe kan 'yan sandan sarauniya ya yi yawa, da suka hada da karbar cin hanci da cin zarafi
  • Solomon Arase ya ce idan kuma ba a rushe aikin jami'an ba, to ya zama wajibi a samar masu da sabbin kayan aiki da zai bambanta su da ainahin 'yan sanda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaban hukumar 'yan sanda (PSC) , Solomon Arase, ya ce akwai bukatar rushe 'yan sandan sarauniya na rudunar 'yan sandan Najeriya ko kuma a basu launin rigunan aiki daban da na sauran ainahin 'yan sandan.

Kara karanta wannan

Harin Filato: Peter Obi da wasu yan siyasa da suka ziyarci wadanda abin ya shafa, sun ba da kudi

A cewarsa, da yawan 'yan sandan sarauniya na aiwatar da ayyukan da basu dace ba, da suka hada da karbar rashawa, wanda ke bata sunan rundunar 'yan sandan Najeriya.

Za a sake fasalin jami'an 'constabulary'.
Hukumar kula da 'yan sanda ta kasa na tattaunawa da babban sufetan 'yan sanda don sake fasalin jami'an 'constabulary'. Hoto: @PSCNigeria
Asali: Twitter

Korafe-korafe kan jami'an kwanstabulari ya yi yawa - PSC

Arase ya bayyana matsayarsa ne a ranar Alhamis ta bakin kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, a cikin wata sanarwa da ya fitar, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Hukumar ta fara tattaunawa da babban sufeta janar na rundunar 'yan sanda kan yiwuwar dakatar da 'yan sandan sarauniya sauya masu kayan aiki.
"Korafe-korafe akan jami'an ya yi yawa, su ne karbar cin hanci da rashawa, su ne cin zarafin mutane, duk abin da za su yi ba ya tafiya dai dai da manufar da aka samar da su."

A rushe aikin jami'an a jihohin da ba a biyansu albashi - PSC

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali bayan direbobin mota sun murkushe jami'an 'yan sanda 2 da gan-gan

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Idan aka zabi a barsu, to dole a canja masu launin rigunan aiki ko kayan aikin gaba daya don ya bambanta su da ainahin jami'an 'yan sanda, wanda zai sa jama'a su rinka gane jami'an.
"Daukar wadannan matakai zai taimaka wajen dakile bata sunan da suke jawo wa rundunar 'yan sanda, haka zalika hukumar na neman a rushe sashen jami'an a jihohin da ba a biyansu albashi ko kula da su"

Hukumar PSC ta ce kuskure ne jihohi su samar da bangaren jami'an tsaro ba tare da suna biyansu ba, wanda ke tilasta su karbar rashawa ko cin zarafin mutane don samun na goro.

Yan 'sandan sarauniya na da nasu muhimmancin - Abubakar

Wani da Legit ta tattauna da shi, Abubakar Ibrahim daga jihar Bauchi ya ce 'yan sandan sarauniya na da muhimmanci a cikin al'umma duk da korafe-korafen da ake a kan su.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 100 a filato, majalisa ta nemi zama da jigogin tsaro

Ibrahim ya ce kaso 60% zuwa 70% na 'yan sandan da ke tsaron titi, ko kama masu laifi 'yan sandan sarauniya ne, kuma ko a ofishin 'yan sanda sukan taka rawar gani.

A cewarsa:

"Suna karbar cin hanci ne saboda ba sa samun albashi, kuma ba cikakkun jami'an gwamnati ba ne, amma da za a rinka ba su albashi, to da za su daina karbar rashawa."

Dalilin da ya sa 'yan sanda ke karbar cin hanci - IGP

A wani labarin, James Oppong-Boanuh, shugaban 'yan sandan kasar Ghana a shekarar 2019, rashin kwarewar aiki ne ke saka 'yan sanda karbar cin hanci daga farar hula.

Shugaban 'yan sandan na lokacin ya ce, masu karya doka na ba 'yan sanda cin hanci don gudun gurfanar dasu, wannan kuwa na kayatar da 'yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel