Yadda Muka Samu Sabani da Uwargidata, Ta Kore Ni a Kan Rarara Inji Fatima Mai Zagole

Yadda Muka Samu Sabani da Uwargidata, Ta Kore Ni a Kan Rarara Inji Fatima Mai Zagole

  • Fatima Mai Zogale ta maida martani bayan jin uwargidarta ta karyata cewa ta sallame ta daga wurin aikinsu
  • Wani ma’abocin shafin Facebook ya wallafa bidiyon bayanin da wannan baiwar Allah ta yi bayan ta rasa aikinta
  • Martanin ya zama dole ne domini ta Hajiya Aisha ta ce yarinyar shagon ce ta bar aiki bayan an rangada mata waka

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Fatima Mai Zogale ta fito ta yi magana bayan kurar da aka tada bayan da aka ji cewa an kore ta daga wurin aikinta.

Tun da Dauda Kahutu Rarara ya yi wa wannan ‘yar kasuwa mai dafa zogale waka, shikenan sai ta shahara a dare daya.

Kara karanta wannan

Minista: 'A dawo da Betta Edu ta cigaba da ayyukan raya kasa', An roki Tinubu

Rarara | Fatima Mai Zogale
Dauda Rarara ya yi wa Fatima Mai Zogale waka a Kano Hoto: Dauda Kahutu Rarara/Insidearewa
Asali: Facebook

Fatima Mai Zogale ta bayyana bangarenta

A wani bidiyo, an ji Fatima Mai Zogale ta yi karin hasken kakkabe kura a sakamakon fitowar kalaman tsohuwar uwar gidarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai zogalen ta karyata abin da uwar gidarta ta fada, inda ta nuna ita ce ta bar aiki a shagon ba wai saboda an fatattake ta ba.

Rigimar Fatima Mai Zogala da Aisha

A cewarta, ba wannan ne karon farko da suka samu sabani da Aisha ba, ta ke cewa da azumi sai da ta kore ta daga wajen aiki.

Abin da ya jawo sabanin kuwa a cewarta, turmin zani ne da aka ba ta kyauta ta dinka tare da mahaifiyarta domin bikin sallah.

Bayan ta dawo aiki saboda an daina ciniki a shagon, sai Fatima Mai Zogale ta ci karo da mawakin nan Dauda Kahutu Rarara.

Kara karanta wannan

Rashin haihuwa: Matar aure ta sayi kayan jarirai, ta wallafa bidiyon halin da take ciki

Kabir Garba da ya daura bidiyon, ya ce lamarin ya bar kura bayan wakar Dauda Rarara a sakamakon cin zogale da ya yi.

Rarara ya hadu da Fatima Mai Zogale

Tun can ta dade tana kaunar Rarara, sai kuma aka yi dace bayan ‘yan kwanaki da cin zogale a wajenta, sai ya yi mata waka.

Mai zogalen ta ce saboda Hajiya Aisha ta ji ba a ambace ta a wakar ba, alhali kuwa ita ce mai shago, wannan abin ne ya fusata ta.

Duk da Fatima ta yi ikirarin ta ba uwar gidarsu hakuri, wannan bai hana daga baya ta sallame daga shagon neman na abincin ba.

A game da zancen aure kuwa, Fatima ta ba da uzuri da cewa komai da lokacinsa, kuma ta kara da cewa an daga ranar aurenta.

Matsalar man fetur a Kano da garuruwa

A baya kun ji labari cewa ba a dade da kukan rashin isasshen da kuma tsadar wutar lantarki ba, ana wahalar man fetur a garuruwa.

‘Yan kasuwa sun fadi inda aka samu matsalar, sun bayyana cewa NNPCL na neman kawo mafita domin a kawar da layi a gidajen mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel