Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya Ta Yi Nasara Yayin da Aka Sanar da Sakamakon Zabe a Gombe

Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya Ta Yi Nasara Yayin da Aka Sanar da Sakamakon Zabe a Gombe

  • Jam'iyyar APC a jihar Gombe ta yi nasara a zaben ƙananan hukumomi 11 da aka gudanar a yau a fadin jihar baki daya
  • Jam'iyyar ta lashe dukkan zabukan da aka gudanar har da na kansiloli a unguwanni 114 a yau Asabar 27 ga watan Afrilu
  • Legit Hausa ta ji ta bakin jigon jam'iyyar PDP a Gombe kan wannan zaben da aka gudanar a jihar a jiya Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Jam'iyyar APC ta lashe dukkan zabukan ƙananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar a jihar Gombe.

Daga cikin wadanda suka samu nasara akwai tsohuwar mamban Majalisar Tarayya, Fatima Binta Bello.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamako: PDP ta lashe zaben dukan kujerun kananan hukumomi 33 a jihar Oyo

APC ta kashe zaben kananan hukumomi da kansiloli a Gombe
Hukumar zabe ta sanar da APC a matsayin wacce ta lashe zaben kananan hukumomi a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Wace jami'yya ce ta lashe zaben a Gombe?

Jam'iyyar ta lashe dukkan zabukan ƙananan hukumomi 11 da na kansiloli 114 da aka gudanar a yau Asabar 27 ga watan Afrilu, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baturen zaben, Sa'idu Awak shi ya sanar da haka bayan kammala zaben da aka gudanar a jihar inda ya ce APC ta lashe zaben ba tare da hamayya ba.

Awak ya ce a zaben karamar hukumar Gombe, dan takarar jam'iyyar APC, Sani A. Haruna shi ya lashe zaben da kuri'u 72,286.

Tsohuwar 'yar Majalisa ta yi nasara

Yayin da mai bi masa a jam'iyyar PDP ya zamo na biyu da kuri'u 1,678 a zaben karamar hukumar.

A kananan hukumomin Kaltungo da Shongom, 'yan takarar jam'iyyar, Iliya Sulaiman Jatali da Fatima Binta Bello sun yi nasarar lashe zaben.

Binta Bello wacce tsohuwar 'yan Majalisar Tarayya ce da ta wakilci yankin mazabar Kaltungo/Shongom ta yi nasara a zaben karamar hukumar Shongom.

Kara karanta wannan

Ganduje: Abba ya shiga matsala bayan APC ta bankaɗo 'makircin' da ake zargin yana ƙullawa

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya taya murna ga dukkan wadanda suka lashe zaben a yau Asabar 27 ga watan Afrilu.

Sakataren yada labaran gwamna, Isma'ila Uba Misilli shi ya tabbatar da haka a yammacin yau Asabar a shafinsa na Facebook.

Tattaunawar Legit Hausa da jigon PDP

Legit Hausa ta ji ta bakin jigon jam'iyyar PDP a Gombe kan wannan zaben da aka gudanar

Kwamred Aliyu Abubakar Abdulkadir wanda ya ke neman kujerar matasan jam'iyyar a jihar ya koka kan yadda aka yi zabe.

Ya ce babu wani zabe da aka yi kawai an dauki daidaikun mazabu ne a ka dauka aka kuma yaɗa a kafofin sandarwa.

"Wasu mazabu ne aka zaba kamar Jekadafari a mazabar gwamna da kuma Bolari wanda anan aka nada ciyaman."
"Kamar a Pantami ba muga ko akwati daya ba, mun je mazabar Pantami tun da safe shiru sai dai idan bayan karfe 5:00 aka kawo, kuma nan mun dawo da dare ba mu ga komai ba."

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

- Kwamred Aliyu Dyer

Ganduje ya kaddamar da hanyarsa a Gombe

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da titin da aka sanya wa sunan sa a jihar Gombe.

Yayin da shugaban jam'iyyar ya ziyarci jihar Gombe domin ayyukan da suka shafi zaben kananan hukumomi, gwamna jihar ya karrama shi da sanya wa titi sunan sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel