Sarauta da Sarauta: Sarakunan Kano da Bichi Sun Hada ‘Ya ‘yansu Auren Zumunci

Sarauta da Sarauta: Sarakunan Kano da Bichi Sun Hada ‘Ya ‘yansu Auren Zumunci

  • Alakar ‘yanuwantaka na jini ya hade da sarauta yayin da ‘dan mai martaba Sarkin Kano ya yi aure a ranar Juma’ar nan
  • Sanusi Aminu Bayero ya angwance da sahibarsa Rumana Nasir Ado Bayero wanda Mai martaba Sarkin Bichi ne mahaifinta
  • Farfesa Sani Zahradeen ya daura auren da Walin Kano ya ba mataimakin gwamna a madadin jikan Marigayi Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - An hada auren zumunci tsakanin ‘yanuwa tsakanin ‘ya ‘yan Sarakunan Kano da na Bichi da ke jihar Kano a makon nan.

Daily Trust ta rahoto cewa yaron Mai martaba Aminu Ado Bayero ya auri diyar Nasiru Ado Bayero a ranar Juma’ar da ta wuce.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata Kuma Dattijon Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Kano

Daurin auren 'ya 'yan Sarkin Kano
Daurin auren Sanusi Aminu Bayero da Rumana Nasir Ado Bayero Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

Yadda aka daura auren 'ya'yan Sarkin Kano

Sanusi Aminu Bayero ya auri Rumana Nasir Ado Bayero a fadar Sarkin Kano da ke birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban limamin masallacin fada, Farfesa Sani Zahradeen ya daura wannan aure da kimanin karfe 10:00 na safiyar jiya.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya tsaya a matsayin wakilin Ango, ya kuma nema masa auren.

Dan Iyan Kano, Ahmad Ado Bayero shi ne waliyyin Amarya Rumana Nasir Ado Bayero.

Kamar yadda bayanai suka zo mana, an ba da auren Rumana Nasir Ado Bayero ga dan uwan na ta ne a kan sadaki N250, 000.

Mahalarta daurin auren Sanusi & Rumana Bayero

Mutane da-dama sun halarci wannan gagarumin aure inda ‘ya ‘yan sarakuna biyu suka sake kulla igiyar dangantaka da mulki.

Shugabannin majalisa Godwill Akpabio da Barau Jibrin da Abbas Tajuddeen sun halarci bikin.

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

Hotuna daga shafin masarautar a dandalin X sun nuna sauran mahalartar sun hada da Sule Lamido, Ali Modu Sheriff da sauransu.

Kano: Takaitaccen bayani kan Ango da Amarya

Angon ya kammala karatun digirinsa a fannin ilmin kula da kasuwanci ne a jami’ar MTI University da ke Masar a shekarar 2020.

Amaryar kuwa ta yi digirinta a harkar gine-gine a wata jami’ar Portsmouth a Birtaniya.

A yau ne kuma aka ji yaron Sarkin Bichi, Abdulkadir Nasir Ado Bayero zai auri diyar tsohon ministan noma, Abba Sayyad Ruma.

Kokarin Daurawa da Hisbah a Kano

A babin addini, an ji labari Aminu Daurawa ya fadi yadda ta kaya tsakaninsa da mutumin da yake buga ashar ana ba shi kudi.

Ana yawo da Umar Bush har a cikin jirgin sama daga gari zuwa gari, shi kuwa yana irin ta maguzawa wanda ya sabawa musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel