Bayan Kashe Mutane Sama da 100 a Filato, Majalisa Ta Nemi Zama da Jigogin Tsaro

Bayan Kashe Mutane Sama da 100 a Filato, Majalisa Ta Nemi Zama da Jigogin Tsaro

  • Majalisar dattawa ta nemi zama da manyan masu jan ragamar tsaron Najeriya don tattauna batutuwan tsaro
  • Wannan na zuwa ne a martaninsu na kai harin da aka yi a jihar Filato a makon da ya gabata, inda aka kashe jama'a da yawa
  • A baya kadan, an kashe wasu mutanen da ke bikin Maulidi a jihar Kaduna, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar nan

FCT, Abuja - A ranar Asabar ne majalisar dattawa ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro kan kisan gillar da aka yi wa mutane sama da 100 a jajibirin Kirsimeti a jihar Filato.

Akalla mutum 145 ne aka kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka 23 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Hare-haren, wadanda kuma suka yi sanadin jikkata daruruwan mutane tare da lalata dukiyoyi, an ce an yi su ne tsakanin daren ranar Asabar zuwa safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

IGP ya yi kus-kus da Gwamna Mutfwang, ya bada muhimmin umurni yayin da ake kashe-kashe a Filato

Majalisa za ta zauna da sojojin Najeriya kan tsaro
Majalisa za ta zauna da jiga-jigan tsaron Najeriya | Hoto: @TopeBrown
Asali: Twitter

Abin da majalisa ke zargi

Majalisar dattijai ta ce duba da yadda ‘yan ta’addan suka kitsa tare da kai harin, ya nuna akwai mishkila ga tsarin bayanan sirrin tsaron Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta gayyaci babban hafsan hafsoshin tsaro, babban hafsan soji, hafsan hafsoshin sojin sama, darakta janar na hukumar tsaro ta SSS da mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro.

Hakazalika, kiran bai bar darakta janar na Hukumar Leken Asiri ta Najeriya da Sufeto Janar na 'yan sanda kan kashe-kashen.

Wannan kuwa ya faru ne a yau Asabar 30 ga watan Disamba a zaman majalisar, inda sanata Diket Plang na APC daga jihar Filato ya dago maganar.

Dalilin da yasa ake son zama da manyan tsaro

Shugabannin jami’an tsaro za su yi wa majalisar dattawa bayani kan munanan kashe-kashen da ake yi a jihar Filato domin baiwa majalisar damar daukar mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fusata kan tsaro, ya tura zazzafan gargadi ga sabbin sojin da suka samu karin girma

Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi), wanda ke jagorantar kungiyar Sanatocin Arewa, ya bayyana harin a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba, rahoton Channels Tv.

Dan majalisar ya ce sakamakon binciken da ya yi bayan shafe sa’o’i 72 a Filato tare da ganawa da gwamnan jihar, ya nuna cewa maharan tare da hadin gwiwar mazauna yankin sun kai hare-haren ne cikin shiri.

Abin takaici ne yadda aka kai harin, inji tsohon gwamna

Ya ce ‘yan bindigan da yawansu ya kai 400, sun gudanar da barnarsu cikin tsari ba tare da wata tsangwama ba, yana mai zargin jami’an tsaron da gaza tabuka komai bayanan da suka samu bayanan sirri kafin a kai harin.

Simon Lalong, wanda tsohon gwamnan jihar Filato ne, ya yi watsi da ikirarin da sojoji suka yi na cewa yankin na da wuyar shiga kasancewarsa yana da nisa da inda sojoji suke.

Ya bayyana rashin jin dadinsa cewa duk da yawan rundunonin soji daban-daban da suka hada da ‘Operation Safe Haven’ na wanzar da zaman lafiya a jihar, ana asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan kashe bayin Allah 195 a jiha ɗaya, miyagu sun sake kai mummunan hari, sun tafka ɓarna

Sojoji sun dakile hari

A wani labarin, hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun dakile haren-haren da aka yi yunƙurin kai wa kauyuka 19 a jihar Filato a ranar 24 ga Disamba, 2023.

A jajibirin Kirsimeti, an tabbatar da mutuwar mutane 195 sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyuka a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel