Jerin 'Yan Siyasar Najeriya da 'Ya'yansu Suka Yi Fito Na Fito da Su

Jerin 'Yan Siyasar Najeriya da 'Ya'yansu Suka Yi Fito Na Fito da Su

Manyan 'yan siyasa da dama a Najeriya sun fuskanci matsala daga iyalansu musamman 'ya'yan cikinsu watakila saboda bambancin ra'ayin siyasa ko neman shugabanci.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A siyasa musamman a Najeriya babu masoyi na din-din-din haka kuma aka ce babu makiyi na har abada.

Jerin 'yan siyasa da 'ya'yansu suka bijire musu
Ganduje da sauran 'yan siyasa da suka samu matsala da 'ya'yansu. Hoto: APC Nigeria, Olusegun Obasanjo, Toyin Saraki.
Asali: Twitter

'Yan siyasa da suka yi gumurzu da 'ya'yansu

Hakan bai rasa nasaba da bambance-bambancen siyasa da ke faruwa wanda ke haddasa gaba ko rashin fahimta a tsakani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta jero musu 'yan siyasa da suka samu matsala da 'ya'yansi kan wasu bambance-bambance.

1. Abdullahi Ganduje vs Abdul'aziz Ganduje

Kara karanta wannan

Buhari ya yi ta'aziyya yayin da tsohon sanata da ɗan uwan tsohon hadiminsa suka rasu a Kano

A kwanan nan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya samu matsala da ɗansa, Abdul'aziz Ganduje inda ya fito fili ya nuna baya tare da mahaifinsa.

An gano Abdul'aziz a ofishin yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ana tsaka da tuhumar tsohon gwamnan jihar kan badakalar kuɗi, cewar TheCable.

Ɗan shugaban jam'iyyar ya nuna goyon bayansa kan binkicen mahaifinsa da ake yi inda ya ce zai ba da dukkan gudunmawa da ake bukata.

2. Iyabo Obasanjo vs Olusegun Obasanjo

Iyabo wacce ita ce 'yar farko ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta rubuta wasika ta musamman ga mahaifinta.

A cikin wasikar, Iyabo ta zargi mahaifinta da neman mulki ta kowace hanya inda ya nemi wa'adi na uku lokacin mulkinsa, cewar Channels TV.

Tsohuwar sanatan ta kuma zargi Obasanjo da watsar da iyalansa da kuma jikokinsa inda ya ke cin zarafin mata.

Kara karanta wannan

Katsina: An shiga makoki bayan 'yan bindiga sun hallaka shugaban APC da wani mutum

3. Bokulo Saraki vs Olusola Saraki

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya zargi mahaifinsa da neman sai kanwarsa ta gaji kujerarsa ta gwamna.

Olusola ya so Gbemisola ta gaji kujerar gwamnan Kwara bayan Saraki ya kammala wa'adinsa a matsayin gwamna jihar, cewar rahoton Vanguard.

Yayin da mahaifin ya gane Saraki ba zai bi umarninsa ba sai ya sauya sheka daga PDP zuwa ACPN inda Gbemi ta ke takardar gwamna.

Daga bisani Saraki ya tsayar da ɗan takara a jam'iyyar PDP, AbdulFatah Ahmed inda ya lashe zaben gwamnan jihar a 2011.

APC ta zargi Abba kan zanga zanga

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta zargi Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da daukar nauyin masu zanga-zanga a birnin Abuja.

Jam'iyyar ta ce a cikin masu zanga-zangar har da 'yan Kwankwasiyya wadanda aka yi musu alkawarin makudan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel