Harin Filato: Peter Obi da Wasu Yan Siyasa da Suka Ziyarci Wadanda Abin Ya Shafa, Sun Ba da Kudi

Harin Filato: Peter Obi da Wasu Yan Siyasa da Suka Ziyarci Wadanda Abin Ya Shafa, Sun Ba da Kudi

Hare-haren da yan bindiga suka kai kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar Filato a kwanan nan na ci gaba da haifar da martani daga yan Najeriya, kuma yan siyasa na ta zarya wajen don nuna tausayawarsu.

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, a kalla gawarwaki 195 ne aka kirga zuwa yanzu na wadanda harin wanda ya faru a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba ya ritsa da su.

Yan siyasa sun ziyarci al'ummar Filato da yan bindiga suka farmaka
Harin Filato: Peter Obi da Wasu Yan Siyasa da Suka Ziyarci Wadanda Abin Ya Shafa, Sun Ba da Kudi Hoto: Peter Obi, Kashim Shettima
Asali: Twitter

Kididdigar adadin wadanda suka mutu ya nuna cewa an kashe mutane 148 a karamar hukumar Bokkos, 19 a karamar hukumar Mangu, sannan 27 a Barkin Ladi. An kona gidaje 1,290 a karamar hukumar Bokkos, sannan aka kona gida daya a karamar hukumar Mangu.

Kara karanta wannan

An samu matsala bayan Hukumar Alhazai ta gaza cike yawan kujerunta dubu 95, an fadi babban dalili

Sai dai kuma, wasu yan siyasa sun ziyarci wajen faruwar lamarin sannan sun bayar da gudunmawar yan kudade. Ga jerinsu a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima na daya daga cikin yan siyasar da suka fara ziyartan kauyukan da yi wa wadanda harin da ya ritsa da su jaje.

Yayin ziyararsa, Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ba za ta huta ba har sai an kama maharan tare da hukunta su.

Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023 shima ya ziyarci wajen da masu gudun hijirar suke sannan ya bayar da gudunmawar naira miliyan 5.

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya kalubalanci gwamnatin tarayya da ta dakatar da kashe-kashe a fadin kasar yayin da yake umurtan mutanen jihar Filato da su bari Allah ya daukar masu fansa.

Kara karanta wannan

"Mutane na zaman jira": Ango ya fasa aurensa yan awanni kafin biki, ko'ina ya hargitse

Bello Matawalle

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, na daya daga cikin yan siyasar da suka ziyarci wajen da harin ya faru kuma ya gana da wadanda harin ya ritsa da su, rahoton Punch.

Matawalle, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya jagoranci hafsoshin tsaro, shugaban rundunar soji Laftanal Janar Taoreed Lagbaja, Shugaban sojin sama, Air Marshall Hassan Abubakar da shugaban sojin ruwa Vice Admiral Emmanuel Ogalla, zuwa jihar ta arewa.

Dr Betta Edu

Wta fitacciyar yar siyasa da ta ziyarci Jos, babban birnin jihar Filato, ita ce Dr Betta Edu, ministar jin kai da kawar da talauci.

Ziyarar ta biyo bayan Allah wadai da harin da Shugaban kasa Bola Tinubu yayi tare da umurnin gaggauta kamo maharan.

Majalisa ta kira shugabannin tsaro

A wani labarin, munji cewa a ranar Asabar ne majalisar dattawa ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro kan kisan gillar da aka yi wa mutane sama da 100 a jajibirin Kirsimeti a jihar Filato.

Akalla mutum 145 ne aka kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka 23 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel