Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga, Sun Kwato Miyagun Makamai a Jihohin Arewa 3

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga, Sun Kwato Miyagun Makamai a Jihohin Arewa 3

  • Gwarazan sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga uku tare da ƙwato miyagun makamai a jihohin Kaduna, Sakkwato da Filato
  • A wata sanarwa da rundunar sojoji ta fitar, ta ce jami'anta sun samu wannan nasara ne ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu
  • Sojojin sun daƙile harin garkuwa da mutane a jihar Kaduna, sannan sun yi wa ƴan bindiga kwantan ɓauna a jihar Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Dakarun Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga uku, tare da dakile yunkurin yin garkuwa da mutane, inda suka cafke biyu a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato.

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Zulum ya ba sojoji shawara kan hanyar da za a kawo karshen rashin tsaro a Borno

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun samu nasarori masu yawa a jihohin Sakkwato, Kaduna da Filato Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Sanarwan ta bayyana cewa sojojin sun samu nasarorin ne a samame daban-daban da suka gudanar ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka samu nasara

A jihar Sakkwato, bayan tattara sahihan bayanan sirri, dakarun sojojin sun yi wa tawagar ƴan bindiga kwantan ɓauna a hanyar da suke wucewa a kusa da kauyen Sarma, karamar hukumar Tangaza.

Bayan musayar wuta, sojojin sun yi nasarar kashe jagoran ƴan bindigan tare da ƙwato bindiga kirar AK-47, alburusai da kuma babur.

Haka nan bayan samun kiran gaggawa, sojoji sun daƙile harin garkuwa da mutane a titin ƙauyen Kasu da ke yankin Kafanchan a ƙaramar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.

Sojojin sun kama masu garkuwar mutun biyu, tare da kwato bindiga ɗaya, alburushi na musamman da harsashi daya, da kuma babur.

Sojoji sun kashe ɗan fashi a Filato

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

Bugu da ƙari a wani samamen kuma sojoji sun kashe ɗan fashi da makami guda ɗaya a shingen binciken ababen hawa na Kaskara a ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Filato.

Dakarun sojojin sun samu wannan nasara ne bayan samun kiran gaggawa kan ayyukan ƴan fashi da makami a kewayen UTC.

Sun kuma ƙwato bindiga ƙirar cikin gida guda ɗaya da kuma wasu makamai masu haɗari daga hannun ƴan fashin.

Ƴan bindiga sun shiga fadar Sarki

A wani rahoton kun ji cewa an shiga fargaba yayin da wasu 'yan bindiga suka farmaki garin Zurmi hedkwatar karamar hukumar Zurmi a Zamfara.

Maharan sun kai harin ne a daren jiya Laraba 24 ga watan Afrilu inda suka kutsa kai fadar Sarkin Zurmi da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel