Malam El-Rufai Zai Kara da Tinubu a Zaben Shugaban Ƙasa a 2027? Gaskiya Ta Bayyana

Malam El-Rufai Zai Kara da Tinubu a Zaben Shugaban Ƙasa a 2027? Gaskiya Ta Bayyana

  • Ziyarar da Nasir El-Rufai ya kai wa jiga-jigan adawa da kuma saɓaninsa da gwamnati mai ci ya sa ana tunanin zai tsaya takara a 2027
  • Duk da wannan raɗe-raɗin, tsohon gwamnan Kaduna bai bayyana aniyar neman kujerar shugaban ƙasa ko ya sanar da barin APC ba
  • Amma Mista Kingdom ya jaddada buƙatar cika yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓa, yana mai cewa Kudu ya dace ta ci gaba da mulki a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Motsin aka ga tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya yi kwanan nan ya jawo ana raɗe-raɗin zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Malam El-Rufai na ɗaya daga cikin manyan ƴan siyasar Arewa da suka goyi bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023 da ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya yi martani kan zargin biyan kudin makarantar 'ya'yansa daga asusun Kogi

Shugaba Tinubu da El-Rufai.
Mista Kingdom ya bayyana cewa Kudu ya dace ta ci gaba da mulki a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Kuma ba a yi mamaki ba lokacin da sunansa ya shiga jerin ministoci to amma hakan bai yiwu ba saboda majalisar dattawa ta ƙi amincewa da shi, lamarin da ake kallo da wata manufa ta siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ɗaukar wani lokaci, tsohon gwamnan ya dawo harkokin siyasa gadan-gadan inda ya gana da jagororin jam'iyyar adawa.

Haka zalika yayin da yake jawabi a wurin wani taro a jihar Borno, El-Rufai, ya saɓawa gwamnatin Tinubu, inda ya ce har yanzun ana biyan tallafin man fetur.

El-Rufai na shirin karawa da Tinubu?

Yunƙurin da El-Rufai ya yi ya sa mutane sun fara raɗe-raɗi musamman a kafafen sada zumunta cewa ya fara shirye-shiryen neman kujerar shugaban ƙasa a 2027.

Amma da yake zantawa da Legit.ng kan lamarin, daraktan kungiyar kare muradan matasa, Ogoegbunam Kingdom, ya nuna cewa har yau El-Rufai bai fita daga APC zuwa wata jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

Zulum ya ba sojoji shawara kan hanyar da za a kawo karshen rashin tsaro a Borno

A cewarsa, El-Rufai bai bar APC ba ballantana kuma ya nuna sha'awar neman wani ofishin siyasa a zaɓe na gaba.

"A matsayin ɗan siyasa, yana da damar haɗuwa da abokansa na wasu jam'iyyu domin tattauna batun gina ƙasa da kawo ci gaba," in ji Mista Kingdom.

Ya ƙara da cewa ya kamata a mutunta yarjejeniyar tsarin karba-karɓa a zaben 2027 ta hanyar tabbatar da yankin Kudu ya ci gaba da riƙe kujera lamba ɗaya.

EFCC zata gurfanar da Sirika

A wani rabarin kun ji cewa EFCC ta shirya za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu a mako mai zuwa.

Hukumar ta kama Sirika ne bisa tuhumar da ta shafi wasu kwangiloli da ya bayar na sama da N8bn ga ɗan uwansa, Abubakar Sirika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel