Dalilin da yasa 'yan sanda ke karbar cin hanci - IGP

Dalilin da yasa 'yan sanda ke karbar cin hanci - IGP

Shugaban 'yan sandan kasar Ghana, James Oppong-Boanuh, ya ce dalilin da yasa farar hula ke hanzarin ba wa 'yan sanda cin hanci ne yasa jami'an 'yan sanda ke nuna rashin kwarewarsu a aiyukansu.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawar gidan rediyon da aka yi dashi mai take Ekosii Sen, a gidan rediyon Asempa FM a ranar Talata.

Shugaban 'yan sandan ya ce, direbobi na karya doka ne tare da bada cin hanci don gudun gurfanar dasu. Wannan kuwa yana kayatar da 'yan sanda, in ji shi.

Oppong-Boanuh ya jaddada cewa, idan masu karya doka suka dena bada cin hanci, 'yan sandan ba zasu bukata, ko kuma karbar cin hancin ba gabadaya.

Ya ce, "Idan dukkanmu muka yanke hukuncin dena bada cin hanci kuma muka amince a mika mu kotu, babu dan sandan da zai saka hannu cikin aljihunka ya kwaso kudi."

DUBA WANNAN: Kishi: Yadda matar aure ta antayawa tsohuwar matar mijinta ruwan zafi a fuska

Idan bamu manta ba, Legit.ng ta ruwaito yadda wata babbar motar daukar kaya, dauke da amfanin gona ta murkushe wasu Keke Napep a jihar Adamawa.

Hakan ya biyo bayan bin motar da 'yan sanda suke yi a kan direban bai basu cin hanci ba.

Direban babbar motar ya yi kokarin tserewa 'yan sandan ne don gujewa basu dan 'abin shan ruwa' kamar yadda suka bukata. Lamarin da ya jawo rasa rayuka da dama inda wasu suka jigata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel