Gwamnan PDP Ya Sanya Dokar Taƙaita Zirga-Zirga Saboda Zaɓen Kananan Hukumomi

Gwamnan PDP Ya Sanya Dokar Taƙaita Zirga-Zirga Saboda Zaɓen Kananan Hukumomi

  • Yayin da ake shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi, gwamnatin Oyo ta taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu
  • A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, gwamnatin karkashin Gwamna Makinde ta ce dokar za ta yi aiki daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma
  • Wannan takaita zirga-zirga dai bai shafi jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Oyo ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta sanar da sanya dokar taƙaita zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne saboda zaɓen kananan hukumomin da za a yi a jihar yau Asabar, 27 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

Gwamna Seyi Makinde na Oyo.
An sanya dokar taƙaita zirga-zirga saboda zaben kananan hukumomi a Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin Oyo ta wallafa a sahihin shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Jumu'a da daddare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka sanya dokar?

Taƙaita zirga-zirgar dai zai taimaka wa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Oyo wajen gudanar da zaben ba tare da wata tangarda ba.

Hukumar zaɓen ta shirya gudanar da zaɓen ciyamomi da kansiloli a ƙananan hukumomi 33 na jihar Oyo daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na yamnacin Asabar.

A sanarwan da ta wallafa a X ranar Jumu'a game da zaɓen, gwamnatin Oyo ta ce:

"Da fatan za a lura da wannan muhimmiyar sanarwa game da hana zirga-zirga a jihar Oyo a ranar Asabar 27, Afrilu 2024."
“Gwamnatin jihar Oyo ta sanya dokar hana zirga-zirga a gobe (yau) Asabar, 27 ga Afrilu, 2024, dokar za ta kasance daga ƙarfe 06:00 na safiya zuwa 4:00 na yamma."

Kara karanta wannan

Ondo: PDP ta sanya ranar fidda gwani, daliget 627 za su rabawa mutum 7 gardama

"Waɗanda za su mana muhimman ayyuka ne kaɗai aka kebe daga wannan doka ta hana zirga-zirga ranar Asabar."

Ƙarancin mai a Sakkwato

A wani rahoton kuma Abubuwan sun ƙara dagulewa yayin da aka fara dogon layi a wurin ƴan bunburutu domin sayen mai a jihar Sakkwato

An tattaro cewa mafi akasarin gidajen mai ba su buɗe ba yayin da ƴan kadan da suka fito aiki suna sayar da lita N900 zuwa N1000

Asali: Legit.ng

Online view pixel