Gwamnan APC Ya Amince da Karin Mafi Karancin Albashi a N70,000? an Gano Gaskiya

Gwamnan APC Ya Amince da Karin Mafi Karancin Albashi a N70,000? an Gano Gaskiya

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa ya amince da karin mafi karancin albashi
  • Gwamna ya ce babu kamshin gaskiya kan abin da ake yadawa kan ya amince da biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi
  • Hakan ya biyo bayan wani bayani da gwamnan ya yi a taro inda ya ke cewa nan ba da jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta fitar da sabon albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamnatin jihar Legas ta yi martani kan jita-jitar da ake yaɗawa na biyan mafi karancin albashi.

Gwamnatin ta ce babu kamshin gaskiya cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince da biyan N70,000 ga ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

"Ku daina tsoma baki a gwamnatina" Gwamna ya gargaɗi tsofaffin gwamnoni

Gwamnan APC ya yi martani kan karin mafi karancin albashi
Gwamnan Babajide Sanwo-Olu ya karyata cewa ya kara mafi karancin albashi a Legas. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: UGC

Mene gwamnatin Legas ta ce kan albashin?

Kwamishinan yada labaran jihar, Gbenga Omotosho shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a shafin Facebook a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omotosho ya ce maganar da ake yaɗawa gwamnan ya kara mafi karancin albashi daga N35,000 zuwa N70,000 ba gaskiya ba ne.

"An yi wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu mummunar fahimta kan cewa ya kara mafi karancin albashi N70,000, hakan bai kamata ba."
"Gwamnan cewa ya yi tun a watan Janairu ma'aikata ke karbar N35,000 na rage radadin tallafi da Shugaba Tinubu ya umarta, inda ya ke cewa masu karbar N35,000 yanzu suna samun N70,000."

- Gbenga Omotosho

Gwamnatin Legas ta gargadi masu jita-jita

Omotosho ya gargadi masu yada irin wannan labaran kanzon kurege da su janye daga aikata haka.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta fitar da sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Kungiyoyin kwadago na son gwamnati ta biya ₦615,000 a wata

Ya ce tun watan Janairu ya ke biyan kudin rage radadi N35,000 inda ya ce maikata da ke karbar N35,000 zuwa N40,000 yanzu suna samun ya kai N70,000.

Gwamnan Ebonyi ya kara albashi

Kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru ya amince da rage kudin rijista a Jami'ar jihar da kaso 10% ga dalibai domin tallafa musu.

Gwamnan Ebonyi ya kuma amince da karin albashi ga malaman Jami'ar da sauran ma'akatansu da kaso 20% a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel