Kamfanonin Dangote, BUA Na Iya Kara Farashin Kaya Saboda Tashin Bakin Mai A Kasar

Kamfanonin Dangote, BUA Na Iya Kara Farashin Kaya Saboda Tashin Bakin Mai A Kasar

  • Kayan masarufi na iya tashin gwauron zabi yayin da ake hasashen litar bakin mai za ta kai Naira 1500
  • Akwai alamun kamfanonin Dangote da BUA su iya kara farashin kayayyakinsu saboda tashin farashin
  • A Najeriya farashin mai na daga cikin abubuwan da ke juya akalar tashi ko saukan farashin kaya

Akwai hasashen ma su kamfanoni za su kara farashin kaya yayin da litar bakin ta doshi Naira 1500.

Wannan na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ta shirya saka tallafin mai bayan gangan mai ta kai Dala 97 Legit ta tattaro.

Dangote, BUA na iya kara kudin kaya saboda tashin farashin mai
Kamfanonin Dangote, BUA Na Iya Kara Farashin Kaya. Hoto: Aliko Dangote, Rabiu.
Asali: Getty Images

Meye zai jawo tashin kaya daga Dangote, BUA?

Masu sarrafa kayayyaki za su iya fuskantar tashin farashi a bangarensu wanda hakan ya sa ake hasashen za su kara farashin kayansu saboda tashin farashin litar danyen man.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnatin Tinubu ta warke, farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta tattaro cewa yadda farashin mai ke tashi ya karu da kaso hudu zuwa biyar a cikin 'yan kwanakin nan wanda hakan na da tasiri a farashin kayayyaki.

Kamfanonin Dangote da BUA na iya kara farashin kayayyaki ganin yadda farashin litar bakin man ke tashi wanda su ke amfani da shi.

Wane hasashe ake kan karin farashin kaya?

Masu hasashe sun tabbatar cewa gangan mai din na iya kaiwa Dala 100 kafin karshen watan Disambar wannan shekara.

Matsalar na karuwa ne yayin da kasar Najeriya ta gagara samar da bakin man wanda ta dogara daga wasu kasashe don shigo da shi.

Gwamnatin Najeriya ta dawo da tallafi bayan cire shi a watan Mayu na wannan shekara.

Mutane sun yi martani yayin da Legit Hausa ta tuntube su kan wannan matsalar da ake ciki.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Siyawa Budurwa Sabuwar Marsandi, iPhone 15 Da Fili, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Sani Muhammad ya ce a gaskiya ya kamata gwamnati ta duba lamarin idan abin ya kara karuwa ba a san ina za a shiga ba.

Salisu Adamu ya ce:

"Ina mamaki wane irin tsari gwamnati ke amfani da shi wurin dakile tashin kaya, ya kamata a sauya tunani."

Muhammad Aliyu ya ce shi a bangarenshi kawai sai dai ya yi addu'a don lamarin kasar ya fita a kansa.

Gwamna CBN ya shirya karya farashin kaya a Najeriya

A wani labarin, sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana himmatuwarshi wurin dakile hauhawan farashin kayayyaki a kasar.

Cardoso ya bayyana haka yayin tantance shi da majalisar Dattawa ta yi a wannan mako da muke ciki a a Abuja.

Ya ce matsalar tashin farashin kayan ba maganan yawa ko karancin kudi ba ne kawai ta shafi bangarori da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel