Majalisar Dattawa Ta Kammala Tantance Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

Majalisar Dattawa Ta Kammala Tantance Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

  • A makon da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya nada Olayemi Cardoso a matsayin mukaddashin bankin CBN
  • Tinubu ya kuma nada mataimakan gwamna na bankin CBN guda hudu da ya hada da Muhammad Dattijo yaron Nasir El-Rufai
  • A yau Talata majalisar ta fara tantance Cardoso don tabbatar da shi a matsayin gwamnan CBN bayan dakatar da Emefiele

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta kammala tantance sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso.

Majalisar ta fara tantance gwamnan ne a yau Talata 26 ga watan Satumba a dakin majalisar da ke Abuja.

Majalisar Dattawa ta kammala tantance gwamnan CBN, Cardoso
Majalisar Dattawa Ta Tantance Olayemi Cardoso. Hoto: @dipoaina1.
Asali: Twitter

Yaushe aka nada Cardoso gwamnan CBN?

Legit ta tattaro cewa an nada Cardoso a matsayin mukaddashin gwamnan CBN a makon da ya gabata kafin tantance shi da majalisar ta yi a yau.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Yemi Cardoso a Matsayin Sabon Gwamnan CBN, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga nadin Cardoso, Shugaba Tinubu ya nada mataimakan gwamnan bankin guda hudu wanda ya hada da yaron Nasir El-Rufai, Muhammad Sani Dattijo.

Har ila yau, Shugaba Tinubu ya nada mataimakan gwamnan CBN, guda hudu wadanda za su shafe wa'adin shekaru biyar, cewar Vanguard.

Nadin nasu zai tabbata ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance su tare da tabbatar da su.

Mataimakan gwamnan CBN din sun hada da Emem Nanna da Mista Philip Ikeazor da Dakta Bala M. Bello da kuma Muhammad Sani Dattijo.

Wanene sabon gwamnan CBN, Cardoso?

Idan ba a mantaba Cardoso ya kama aiki ne a matsayin mukaddashin Babban Bankin Najeriya, CBN a makon da ya gabata.

Cardoso ya kasance na kusa ga Shugaba Tinubu wanda aka haifeshi a ranar 10 ga watan Yuli a shekarar 1957.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Saka Ranar Tantance Gwamnan CBN, Mataimakansa Da Wasu Ministoci 2

Ya halarci makarantar Kwalejin St. Gregory ya kuma samu shaidar kammala digiri dinsa a Jami'ar Aston da ke birinin Birmingham a kasar Ingila.

Cardoso ya kuma kammala karatun digirin digirgir a Jami'ar Harvard a bangaren gudanarwa.

Cardoso ya fara aiki a matsayin gwamnan CBN

A wani labarin, sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya fara aiki a hukumance a matsayin gwamnan bankin.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada shi bayan dakatar da Godswin Emefiele.

Tinubu ya kuma nada mataimakan gwamnan bankin CBN guda hudu a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.