Saurayi Ya Gwangwaje Budurwa Da Sabuwar Marsandi, iPhone 15 Da Fili, Ta Rusa Ihu a Bainar Jama’a

Saurayi Ya Gwangwaje Budurwa Da Sabuwar Marsandi, iPhone 15 Da Fili, Ta Rusa Ihu a Bainar Jama’a

  • Wata matashiyar budurwa ta yi gamon katar yayin da saurayinta ya siya mata sabuwar mota kirar Marsandi GLE don murnar zagayowar ranar haihuwarta
  • Baya ga sabuwar motar ya hada mata da sabuwar wayar iPhone 15 da fili domin ta gina gida
  • Masu fatan alkhairi sun kewaye matashiyar yayin da ta zauce saboda tsananin murnar samun sabuwar mota ja

Wata matashiyar budurwa ta rusa ihu sannan ta kusa shidewa bayan ta ga sabuwar motar Marsandi da saurayinta ya siya mata a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarta.

An saka motar kirar Marsandi a cikin wani jan kwali. Ta kusa zaucewa a lokacin da aka mika mata makullin yayin da kawayenta suka bukaci ta saita kanta wuri daya.

Saurayi ya gwangwaje budurwarsa da kyaututtuka
Saurayi Ya Gwangwaje Budurwa Da Sabuwar Marsandi, iPhone 15 Da Fili, Ta Rusa Ihu a Bainar Jama’a Hoto: @mckpolokpolo1
Asali: TikTok

Wayar iPhone 15 da Marsandi GLE a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwa

A cewar @mckpolokpolo1, wacce ta yada bidiyon, saurayin nata ya siya mata wayar iPhone 15 da kuma fili.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yi gaggarumin biki ne na gabatar da wadannan kyaututtuka. Ana ta ihun murna ta ko'ina yayin da masu fatan alkhairi suka jinjina irin farin cikin da matashiyar ta yi a bidiyo.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Edwin ya ce:

"Tsafi ya yi aiki a jikin Odogu shakka babu."

swagger_MBR ya ce:

"Ka kaddara Odogu ya fito ya ce zolaya ce."

Students Journalist.. ta ce:

"Odugu ya san abun da zai samu a matsayin tukwici."

Choice ta ce:

"Ya ubangiji na ga abun da kake yi wa sauran mutane saurayina na da zuciyar bayarwa don Allah ka albarkace shi fiye da tsammani don ya yi mani fiye da haka."

Big Rukylex ta ce:

"Na rako sauran yan mata duniya ne."

Denny ta ce:

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Gwamnan CBN Ya Sha Alwashin Dakile Tashin Farashin Kaya, Ya Fadi Dalillai

"Idan har da gaske ne na roki Allah ya yi mani irin haka sannan ya yi maki fiye da haka."

Tsohon direban tasi a Najeriya ya koma Kanada, ya siya mota cikin kwana 10

A wani labarin, wani mai aikin gini a Najeriya mai suna, @MRBRIKILA1, ya garzaya shafin soshiyal midiya don murnar siyan sabuwar mota kasa da makonni biyu bayan ya koma kasar Kanada.

@MRBRIKILA1 ya wallafa hotunan sabuwar motarsa kirar Honda Odyssey, a shafin X yana mai bayyana cewa ya isa Kanada a ranar Juma'a sannan ya fara aiki a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel