Sabon Gwamnan CBN, Cardoso Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Tashin Farashin Kaya

Sabon Gwamnan CBN, Cardoso Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Tashin Farashin Kaya

  • Da alamu sauki zai samu a Najeriya bayan sabon gwamnan bankin CBN ya yi alkawarin kawo karshen tashin farashin kaya
  • Olayemi Cardoso ya bayyana haka ne yayin da ake tantance shi a Majalisar Dattawa a jiya Talata 26 ga watan Satumba
  • Cardoso ya ce matsalolin da su ke jawo tashin farashin kayayyaki a kasar su na da yawa wanda dole a shawo kansu

FCT, Abuja - Sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana shirinsa na kawo karshen hauhawan farashin kaya.

Cardoso ya kuma bayyana himmatuwarshi wurin kawo karshen yawan cire kudade da bankin ke yi ga jama'a, Legit ta tattaro.

Gwamnan CBN, Cardoso ya yi alkawarin kawo karshen tashin farashin kaya
Gwamnan CBN, Cardoso Ya Yi Kan Tashin Farashin Kaya. Hoto: CBN.
Asali: Facebook

Wane alkawari gwamnan CBN ya yi?

Gwamnan bankin ya bayyana haka ne yayin tantance shi da Majalisar Dattawa ke yi a jiya Talata 26 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A kan maganar tashin farashin kayayyaki a kasar, wasu su na cewa rashin tsari ne yayin da wasu ke cewa yanayin samar da kudade ne.
"Maganar gaskiya ita ce matsalar ta shafi dukkan abubuwa guda biyun.
"Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin shekaru 10 zuwa 15, kaso 50 na tashin farashin kaya ya samu ne daga matsalar yawaitar kudi a kasar.

Wane mataki gwamnan CBN zai dauka?

Ya kara da cewa:

"Wannan babbar matsala ce wacce dole mu tinkare ta da karfi don kawo karshen wannan matsalar."

Cardoso ya yi alkawarin cewa CBN zai yi duk mai yiyuwa don ganin matsalar rashin kudi bai zama matsala ba a kasar, Thisday ta tattaro.

A jiya Talata 26 ga watan Satumba ne aka kammala tantance sabon gwamnan CBN, Olayemi Cardoso bayan nadin da Tinubu ya masa a makon jiya.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Za Su Fara Siyan Litar Fetur Kan Naira 180" Malami Ya Hango Sauki, Ya Fadi Lokaci

A satin ne kuma Shugaba Tinubu ya nada mataimakan gwamnan CBN guda hudu na wa'adin shekaru biyar bayan tantance su a majalisa.

Majalisar Dattawa ta tantance gwamnan CBN, Cardoso

A wani labarin, Majalisar Dattawa ta kammala tantance sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso a dakin majalisar.

Shugaba Tinubu ya nada Cardoso a makon da ya gabata inda ya maye gurbin tsohon gwamnan, Godwin Emefiele.

Tinubu ya kuma nada mataimakan gwamnan bankin CBN guda hudu da za su yi wa'adi har na tsawon shekaru biyar bayan tantance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.