Babbar Magana Yayin da Farashin Danyen Man Fetur Ya Tashi a Kasuwar Duniya

Babbar Magana Yayin da Farashin Danyen Man Fetur Ya Tashi a Kasuwar Duniya

  • An samu karin farashin danyen man fetur a duniya, lamarin da ke kara daukar hankali a yanzu kenan
  • Najeriya za ta kara samun kudaden shiga sakamakon tashin farashin danyen man fetur a kasuwar duniya
  • An janye tallafin man fetur, ana fargabar tashin danyen mai zai kara ta'azzara farashi a Najeriya

Farashin danyen danyen mai a kasuwar duniya ya tashi da 3.6% zuwa dala 97 kan ganga guda; sama da dala 94.30 da aka siyar da shi a kasuwar a ranar Litinin da ta gabata.

Tashin farashin danyen man na yanzu ya kuma nuna tashi mafi girma da aka gani tun Nuwamban 2022, TheCable ta ruwaito.

An ce tashin farashin ya ne sakamakon karancin yawan danyen a Amurka, wanda ya kara dagula lamurra kan tsauraran hanyoyin hada-hadar man daga mambobin kungiyar OPEC.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

Danyen mai ya tashi a kasuwar duniya
Yadda farashin danyen mai ya tashi a Najeriya | Hoto: indiatimes.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda man Texas ya tashi

A gefe guda kuma, danyen man Texas da aka fi sani da WTI ya tashi da 2.4% akan dala 93.92 a ganga gida; bayan da ya haura sama zuwa dala 95 a baya a karon farko tun watan Agustan 2022.

Alkaluman gwamnati sun nuna cewa samun danyen man fetur na Amurka ya yi kasa da ganga miliyan 2.2 a makon jiya, inda aka samu ganga miliyan 416.3, rahoton Reuters.

A ranar 5 ga Satumba, 2023, Saudiyya da Rasha sun gama kai don tsawaita rage yawan man da suke hakowa a hade da ganga miliyan 1.3 a kowace rana har zuwa karshen shekara.

Yadda lamarin yake ga Najeriya

A Najeriya, an ce karin farashin danyen danyen man wanda shi ne babbar hanyar samun kudin kasar, tashin farashin zai kara samar da kudaden shiga ga tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An nemi Tinubu ya fadi nawa tara bayan cire tallafin mai, kuma nawa ya kashe

Sai dai kuma hakan ya haifar da fargabar ko tashin farashin danyen man zai shafi farashin man fetur a Najeriya.

Idan baku manta ba, an cire tallafin mai a Najeriya, wanda hakan ke kara ta'azzara lamurra da dama a kasar.

Ya zuwa yanzu, rahoto ya ce gwamnatin Tinubu ta biya wasu adadin kudade duk da cewa an cire tallafin na man fetur a Najeriya tun watan Mayun da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.