Akpabio Ya Bayyana Yadda Emefiele Ya Yi Wa Zaben 2023 Zagon Kasa

Akpabio Ya Bayyana Yadda Emefiele Ya Yi Wa Zaben 2023 Zagon Kasa

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya zargi tsohon gwamnan CBN da shirya maƙarƙashiyar gurugunta zaɓen 2023
  • Akpabio ya yi zargin cewa Emefiele ya kawo tsarin sauya fasalin takardun kuɗi ne domin gurgunta babban zaɓen 2023
  • Shugaban majalisar ya gargaɗi sabon gwamnan CBN, Yemi Cardoso da ya kiyayi shiga harkokin siyasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sake fasalin takardun kuɗin naira da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ɓullo da shi, kafin zaɓen da ya gabata, ya yi shi ne domin kawo cikas ga babban zaɓen 2023.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Akpabio ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 26 ga watan Satumba, wajen tantance sabon gwamnan CBN, Olayemi Cardoso.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Yemi Cardoso a Matsayin Sabon Gwamnan CBN, Bayanai Sun Fito

Akpabio ya fadi manakisar da Emefiele ya shirya
Akpabio ya zargi Emefiele da shirya gurgunta zaben 2023 Hoto: Godswill Obo Akpabio
Asali: Facebook

Shugaban majalisar ya kuma gargaɗi sabon gwamnan na CBN da shiga cikin harkokin da suka danganci siyasa.

Wane irin zargi Akpabio yake yi wa Emefiele

Akpabio ya kuma ce tsohon gwamnan na CBN ya shirya manaƙisa wajen kawo cikas ga babban zaɓen 2023 da ya gabata, rahoton Aminiya ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kazalika ya ce babu ƙasar da ta taɓa sauya fasalin kuɗinta tana shirin shiga babban zaɓe.

Ko da yake bai ambaci sunan Emefiele ba, amma a bayyana yake cewa da tsohon gwamnan na CBN yake.

A kalamansa:

"Gwamnan CBN, ko za ka tsaya tsayin daka wajen bijirewa idan ƴan siyasa suka zo maka don ka shiga takarar shugaban ƙasa ka riƙa nuna hotunan ka ko da kana matsayin gwamnan CBN a taron siyasa?
"Shin za ka yi gaggawar yi wa zaɓukan Najeriya zagon kasa ta hanyar yin sabon takardun kudi, kwanaki biyu kafin zaɓe, yayin da babu wata ƙasa a duniya da ta canza takardun kuɗi a cikin shekara ɗaya, za ka yi naka cikin kwanaki 14 ko 11 don ganin yadda za ka zagon ƙasa ga zaɓe Najeriya?"

Kara karanta wannan

Shugabar Karamar Hukumar da Ya Zargi Gwamnan APC da Wawure Kuɗi Ya Shiga Sabuwar Matsala

Majalisa Ta Kammala Tantance Cardoso

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta kammala tantance sabon gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso.

Majalisar ta kuma amince da naɗin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa tare da mataimakan gwamnan CBN mutum huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng