'Leah Sharibu ta mutu', in ji wata mata da ke hanun 'yan Boko Haram

'Leah Sharibu ta mutu', in ji wata mata da ke hanun 'yan Boko Haram

Grace Taku, ma’aikaciyar agaji da yan Boko Haram suka sace a ranar 18 ga watan Yuli, tayi ikirarin cewa yan ta’addan sun kashe Leah Sharibu tare da wata Alice saboda gwamnatin tarayyar Najeriya taki yin wani abu akai.

Leah Sharibu ta kasance daga cikin yaran makarantar Dapchi 110 da yan ta’addan suka sace a jihar Yobe.

Ta kasance kirista guda a cikin wadanda yan ta’addan suka ki saki bayan gwamnatin tarayya ta tattauna akan sakin sauran.

Taku tayi ikirarin ne a wani sabon bidiyon da yan ta’addan suka saki a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasan arewa sun nuna rashin amincewa da sunayen ministocin Buhari, sun fadi dalili

A cikin bidiyon an jiyo tana fadin: “Sunana Grace, Ina aiki tare hukumar da ke yakar yunwa, wata kugiyar agaji a jihar Borno, sansanina na Damasak. Mun je aiki a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuli 2019. A hanyarmu ta komawa Damasak ta yankin Keneri/Chamba, sai wasu runduna da ake kira Kaliphas suka kama mu sannan suka kawo mu nan. Bamu san inda muke ba.

“Ina roko a madadin dukkaninmu. Bana son hakan abunda ya faru da Leah da Alice ya faru da mu. Saboda Najeriya ta kasa yin komai akansu, ba a sake su ba, an kashe su.”

Ga bidiyon a kasa:

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng