Minista Wike Ya Kori Shugabannin Hukumomi da Kamfanonin FCTA 21, Ba a San Dalili Ba

Minista Wike Ya Kori Shugabannin Hukumomi da Kamfanonin FCTA 21, Ba a San Dalili Ba

  • Minista Wike ya sake barota a Abuja, ya dakatar da wasu manyan jiga-jigai a hukumar FCTA da ke aiki a birnin
  • An ruwaito cewa, ya dakatar dasu nan take, amma bai bayyana ainihin dalilin wannan aiki na rana tsaka ba
  • Tun farkon ba shi ministan Abuja ake ci gaba da cece-kuce da kai ruwa rana da tsohon gwamnan na jihar Ribas

FCT, Abuja - Nyesom Wike ya sake zuwa da batun da zai jawo cece-kuce a Najeriya, ya yi kakkaba tare da korar wasu manyan ma'aikata a hukumar kula da lamurran babban birnin tarayya Abuja.

Raahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wike ya yi wannan korar ne a ranar Laraba 27 ga watan Satumba mai karewa na wannan shekarar.

Ya zuwa yanzu, rahoton da kuma sanarwar da ministan ya fitar bai bayyana gaskiyar dalilin da yasa aka yi wannan dakatarwa ba.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

Wike ya bayyana wannan dakatrwa ta gaggawa ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishinsa, Anthony Ogunleye ya fitar a ranar Laraba, rahoton Channels Tv.

Wike ya yi kora a Abuja
Wike ya kori manyan ma'aikatan FCTA | Hoto: FCTA/Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ta naqalto yadda ya umarci wadanda abin ya shafa da su mika al’amuran gudanarwar ofisoshinsu ga manyan jami’ai masu da ke aiki tare dasu.

Jerin wadanda Wike ya dakatar

1. MD/CEO na sashen kamfanin zuba hannun jarin Abuja investment Company Ltd

2. CEO/MD na gudanarwar kasuwanni a karkashin Abuja Markets Management Ltd

3. MD/CEO na Kamfanin Sufurin Birni na Abuja

4. CEO/MD harkar gidaje da filaye na Abuja Property Development Company

5. CEO/MD na birnin zamani Abuja Technology Village Company Zone Free Trade Zone

6. CEO/MD na Abuja Film Village International

7. CEO/MD na Powernoth AICL Equipment Leasing Company Ltd

8. MD na sashen yada labaran Abuja Broadcasting Corporation

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

9. MD na Abuja Enterprise Agency

10. GM na ma’aikatar ruwan FCT Water Board

11. DG, Hukumar ba da agajin gaggawa ta FCT

12. Babban Sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko ta FCT

13. Darakta Janar na hukumar kula da asibitoci

14. Daraktan hukumar kare muhalli ta Abuja

15. Daraktan hukumar ba da tallafin karatu ta FCT

16. Daraktan hukumar jin dadin alhazai ta FCT

17. Daraktan hukumar jin dadin alhazai kiristoci ta FCT

18. Kodinetan Abuja Infrastructure Investment Center

19. Daraktan ma’aikatar tsarin inshorar lafiya na FCT

20. Kodinetan sashen Satellite Towns Development Department

21. Kodinetan Abuja Metropolitan Management Council

Daga hawa minista Wike ya fara tafiyar da abubuwa

Tun ba shi mukamin minista Wike ke ta kokarin kawo sauye-sauye ga tsaruka da yadda ake tafiyar da lamurra a babban birnin tarayya Abuja.

A baya kunji yadda minista Wike ya soke lasisin filayen wasu jiga-jigan siyasar Najerya a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoto ya bayyana cewa, ma'aikatar ta Wike ta zargi 'yan siyasar, ciki har da Peter Obi da saba ka'ida wajen mallakar filayen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel