Yanzu-yanzu: Leah Sharibu ta haifawa wani kwamandan Boko Haram 'da namiji
Leah Sharibu, yar budurwar da yan Boko Haram suka sace a makarantar Dapchi ta haifi 'da namiji ga daya daga cikin kwamwandojin yan ta'addan. Sahara Reporters ta ruwaito.
Leah ta dauki cikin yaron ne tsawon watanni yanzu bayan an tilasta auren daya daga cikin kwamandojin Boko Haram, a cewar majiya mai siqa na kusa da kungiyar.
Majiyan ya ce ta haifi yaron ranar Asabar a kasar Nijar.
Majiyan ya kara da cewa bayan Leah Sharibu ta ki barin addininta na Kirista, yan Boko Haram sun tilasta masa karba addinin Musulunci kafin aurar da ita. Daga baya sun niyyar sakinta, amma ta kasa tafiya saboda tana dauke da juna biyu. Daily Trust ta ruwaito.
Leah Sharibu na daya daga cikin dalibai matan da yan Boko Haram suka sace a makarantar gwamnatin Dapchi a watan Febrairu, 2018.
DUBA NAN Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da bullar zazzabin Lassa a jihar
A ranar 19 ga Febrairu, 2018, yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun sace yan matan 110 a makarantar mata GGSTC dake garin Dapchi, Bulabulin a karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.
Amma a ranar 21 ga Maris 2018, gwamnatin tarayya ta sanar da cew ayan Boko Haram sun saki yan mata 104 cikin 110 da suka sace a Dapchi, wata yarinya da wani yaro da suka tsinta a hanya.
Biyar daga cikin yan matan sun mutu sakamakon cinkoso yayinda suka rike Leah Sharibu saboda ta ki ridda daga addininta na Kirista.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng