An Bankado Wasikar Da El-Rufai Ya Rubutawa Buhari, Yana Sanar Da Shi Shirin Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Kaduna

An Bankado Wasikar Da El-Rufai Ya Rubutawa Buhari, Yana Sanar Da Shi Shirin Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Kaduna

  • Wata wasika da gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rubutawa Shugaba Muhammadu Buhari ta ce yan ta'addan Ansaru sun fara samun gindin zama a Kaduna
  • El-Rufai ya sanar da Buhari cewa yan ta'addan sun fara kafa 'gwamnatin' su a yankunan karkara inda suka haramta harkokin siyasa, suke harbar haraji da yi wa al'umma shari'a
  • Takardar ta kuma bayyana cewa rahotannin sirri da wayoyin yan ta'adda da ake ji ya nuna cewa suna son kafa sansaninsu na dindindin na shiyar arewa maso yamm a cikin dazukan Jihar Kaduna

Yan ta'adda suna kara samun gindin zama a garuruwan Kaduna tare da kafa 'gwamnati' da 'sansani na dindindin' a jihar ta Arewa maso yamma kusa da babban birnin tarayya Abuja, Gwamna Nasir El-Rufai ya fada wa Shugaba Muhammadu Buhari, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano

El-Rufai
El-Rufa'i Ya Rubutawa Buhari Wasika, Ya Sanar Da Shi Shirin Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Kaduna. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

El-Rufai ya gargadi shugaban game da kaka-gida da yan ta'addan ke yi cikin wata takardar gwamnati da ya aike a karshen watan Yuli, da Premium Times ta gani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yi imanin cewa yan ta'addan na kungiyar Ansaru al-Musulmina fi Bilad al-Sudan, ko Ansaru, sun dawo Birnin Gwari ne a Kaduna a 2012 lokacin da suka balle daga Boko Haram.

A cewar rahotannin sirri da majiyoyi daga mutane da aka tuntuba kan wannan rahoton, yan ta'addan da suka kafa Ansaru ne suka kai manyan hare-hare da Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa kafin su rabu.

Irin hare-haren sun hada da harin ginin majalisar dinkin duniya, UN na watan Agustan 2011 da sace wasu yan kasashen waje. A cewar majiyoyin, Ansaru sun yi mubaya'a ga Al-Qaeda a Islamic Mahgreb, AQIM, a 2020, kuma sune suka yi manyan sace-sace da kaiwa yan sanda hari a Kaduna.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Amma masu bincike da sulhu da suka fahimci yadda yan ta'addan ke harkokinsu sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu akwai hadin kai da ake tsakanin kungiyoyin ta'addanci kamar Boko Haram na ainihi - wato JAS, -ISWAP, Ansaru da yan bindiga.

A 2021, mutum 1,192 ne suka rasa rayyukansu a jihar Kaduna saboda yan bindiga, yan ta'adda da rikici tsakanin garuruwa, muggan hare-hare da harin ramuwar gayya. A cikin wata shida na farkon 2022, mutum 645 sun rasa rayyukansu a yanayi mai kama da wannan a jihar, a cewar gwamnatin jihar.

A takardar da El-Rufai ya rubuta karshen watan Yulin, ya bayyana karara yadda yan ta'addan suka ratsa cikin mutane har suka yi mamaye garuruwan kuma suka kafa 'gwamnatisu mai iko' da ke kula da harkokin zamantakewa da tattalin arziki da yin dokoki da shari'a a yankunan.

Ya ce yan ta'addan sun yi nisa a shirinsu na mayar da dajin Kaduna matsayin 'sansaninsu na dindindin' na yankin arewa maso yamma, yana mai kafa hujja da 'rahotanni na sirri'.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Masu Safarar Kwayoyi da Yan Bindiga Sama da 100 a Jihar Arewa

"Zirga-zirga da aka lura da su tare da sakonni da hukumomin sirri suka gano sun nana karara cewa yan ta'addan na son kafa sansani, a dazukan jihohin Kaduna da Niger," ya rubuta.

Dokar Hana Harkokin Siyasar 2023

A yayin da guguwar siyasa ke kara karfi gabanin zaben 2023, yan ta'addan, El-Rufai ya fada wa Buhari, cewa sun kafa dokar haramtawa mazauna garin shiga harkokin siyasa.

"Yan ta'addan sun kafa doka a yankin, na hanna dukkan harkokin siyasa ko kamfen gabanin zaben 2023, musamman a kauyukan Madobiya da Kazage," gwamnan ya rubuta.

Dama an san yan ta'addan na Ansaru da tsatsauran ra'ayi kan demokradiyya da hukumomin gwamnati wacce bata musulunci ba.

A 2021, a mazabu biyu cikin 11 kawai a Birnin Gwari aka yi kidaya saboda barazanar yan bindiga da yan ta'adda, jami'an jihar Kaduna da hukumar kidaya suka fada wa Premium Times.

An haramta harkokin siyasan ne bayan wani daurin aure da aka yi na baya-bayan nan da yan ta'addan a cewar gwamnan.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

"A cewar bayannan sirri, mambobin Jama’atu Ansarul Musulmina Fi’biladis Sudan (aka Ansaru) da ke zaune da yankin Kuyello a karamar hukumar Birnin Gwari inda suka auri mata guda biyu mazauna kauyen Kuyello," El-Rufai ya rubuta.
"Mambobin kungiyar Ansaru da dama sun hallarci daurin auren kamar yadda mutanen yankin suka shaida. Bayan auren, yan ta'addan, an rahoto sun dauki matan sun tafi da su dajin Kuduru, a yankin."

Karbar Haraji

A bangaren yin shari'a, El-Rufai ya ce yan ta'addan sun "ci tarar wani Mu'azu Ibrahim, mazaunin Kuyello tarar naira miliyan daya saboda sayar da filaye ba tare da izinin masu filin ba."

Bugu da kari, El-Rufai ya ce rashin hukumomin gwamnati a kauyuka yasa yan ta'addan sun nada kansu shugabanni suna karbar haraji daga wurin mutane.

"Akwai rahotanni da dama da ke nuna yan ta'addan na karbar harajin bada tsaro ga manoma da mutanen gari, don basu damar zuwa gonakinsu su yi noma," a cewar gwamnan.

Kara karanta wannan

Babban kamu: Mata 7 da ke kai wa Boko Haram kayan abinci sun shiga hannu a Borno

Masu bincike kan ta'addanci sun ce haraji daga aka kakabawa wasu garuruwan - saboda gazawa ko karancin hukumomin gwamnati - na cikin manyan hanyoyin samun kudin shiga na yan ta'addan.

Kamar yadda El-Rufai ya yi bayani a Kaduna, yan ta'addan ISWAP a yankin Tafkin Chadi suma suna karbar haraji mai tsoka daga hannun masunta da manoma a yankin.

Da aka tuntubi El-Rufai don ji ta bakinsa, ya ce ba zai yi tsokaci kan labarin ba domin wasikar ta sirri ne tsakaninsa da shugaban kasa.

A shekarar 2016, El-Rufai ya taba rubuta irin wannan wasikar ta sirri ga shugaban kasa, yana gargadin cewa farin jinin Gwamnatin Buhari ya fara raguwa shekara guda bayan hawa kan mulki.

Yadda Boko Haram, ISWAP da Ansaru ke haɗin gwiwa da shugabannin ƴan bindigan arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin ta'addanci na Jama’atu Ahlul Sunnah lid Da’awatu wal Jihad (Boko Haram) da Islamic State in West Africa Province (ISWAP) da Jama’atu Ansarul Muslimina fii Biladis Sudan (da aka fi sani da Ansaru) suna gasar neman mabiya daga cikin 'yan bindiga da ke adabar jihohin arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

Kwararru a bangaren tsaro da mazauna yankunan da suka yi magana da wakilin Daily Trust sun tabbatar da cewa kungiyoyin ta'addancin tuni sun fara samun nasara a wannan yunkurin inda wasu daga cikin shugabannin yan bindigan sun fara musu mubaya'a ko aiki tare da musayar bayanai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel