Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

  • Ana ta shan bukukuwa ta kowani bangare na kasar nan kuma wannan karon abun ya yi karfi a bangaren masu hannu da shuni
  • Hotunan wani ango, Abudul'aziz Babaji da kykkyawar amaryarsa, Aisha ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu
  • Tsantsar kyawun ma'auratan shine babban abun da ya ja hankalin mutane, wasu sun hango irin kyawawan yaran da za su haifa tare

A karshen makon jiya ne aka daura auren wani kyakkyawan ango mai suna Abdul’ziz Babaji da hadaddiyar amaryarsa Aisha Aliyu Othman.

Hotunan ma’auratan ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda suka yi shigarsu ta sabbin aure mai cike da kamala.

Amarya da ango
Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya Hoto: arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Sai dai tsantsar kyawu da suke da shi shine abun da ya fi jan hankalin mabiya shafukan soshiyal midiya, harma wasu na hango yadda zuri’ar da za su samu a gaba za su kasance.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

A cikin wasu hotuna da shafin arewafamilyweddings ya wallafa a Instagram, an gano kyakkyawar amaryar tare da angonta suna kallon junansu cike da shauki da soyayyar juna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli hotunan nasu a kasa:

Martanin jama'a

lubbywurno ta yi martani:

"Masha Allah…an zuba kyawu a nan …. amma idan mutane irin haka suka hadu suka auri junansu… Me zai faru da saura ….wa zai aure su"

humairah.ayshat ta ce:

"Masha Allah "

i_am_temmy_ ta ce:

"Duk yan arewar nan kyau ne da su ta koina ina bukatar dan arewa fa"

mnb_kidsnmore ta ce:

"Sun yi kyau matuka. Kyawawan yara na a hanya "

sherieyybeauty ta ce:

"Masha Allah "

p.e.a.c.e_ak ya ce:

"Gsky anye shouck dena"

khadeejerh_ms ta ce:

"Masha Allah "

miemieluv1 ta yi martani:

"Su duka masu keu masha Allah"

Auren Sarauta: Dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

A gefe guda, Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, zai angwance da kyakkyawar amaryarsa.

Yariman ya tsallake jiharsa ta Kano inda ya lula jihar Sokoto wajen zakulo zukekiyar amaryarsa mai suna Aisha Ummaran Kwabo.

Aisha ta kasance diya a wajen Jarman Sokoto, Alhaji Dr Ummaran Kwabo kuma tuni katin gayyatan auren nasu ya yadu a shafukan soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel