Hotunan Yadda Sojoji Suka Kama Wasu Mata da Ke Jigilar Kaya Ga Boko Haram

Hotunan Yadda Sojoji Suka Kama Wasu Mata da Ke Jigilar Kaya Ga Boko Haram

  • Rundunar sojin Najeriya ta cafke wasu mata da ake zargin 'yan Boko Haram ne dauke da kayayyakin zargi
  • Majiyar tsaro ta shaida yadda 'yan ta'adda ke fakewa suna shiga da kayayyaki dazukan da suke buya a yankin
  • Jihar Borno na daya daga cikin jihohin da ke fama da barnar 'yan ta'adda tsawon shekaru sama da 10 kenan

Dakarun Bataliya ta 195 na Operation Hadin Kai, sun cafke wasu mutum 7 da ke jiglar kaya ga 'yan ta'addan Boko Haram a wajen Maidugiri, babban birnin jihar Borno.

Wadanda aka kama sun hada da; Hadiza Ali, Kelo Abba, Mariam Aji, Kamsilum Ali, Ngubdo Modu da Abiso Lawan, da dai sauransu, Leadership ta ruwaito.

An kama wasu mata 'yan Boko Haram guda 7 a Borno
Hotunan yadda sojoji suka kama waus mata da ke jigilar kaya ga Boko Haram | Hoto: Leadership News
Asali: Facebook

A cewar wani rahoton sirri da Zagazola Makama ya samu daga manyan majiyoyin soja, an gano wadanda ake zargin dauke da tarin kaya da aka tanada domin kai wa ‘yan ta’addar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A yayin binciken, an gano kayayyaki daban-daban da suka hada da man fetur mai yawa, gidajen sauro, taliya da sauransu.
“Sai dai sojoji sun shiga shakku a lokacin da aka ga garri da yawa da aka boye a cikin galan a karkashin motocin.
“Bayan an yi musu tambayoyi, matan sun amsa cewa ‘yan Boko Haram ne da ke barna a sansanin IDP na Muna Garage, Mafa da Dikwa tare da mayakansu a sansanin Boboshe da Gulumba a karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

Sun bayyana cewa, sun cika jarakunan da gari ne saboda kaicewa zargin sojojin da ka iya tare su a hanya su bincike su.

Ya zuwa yanzu dai jami'an sojin Najeriya na ci gaba da kai farmaki maboyar 'yan ta'adda a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Yan 'Boko Haram' Sun Kai Hari Hedkwatar Ƴan Sanda A Kano, Sun Yi Harbe-Harbe

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

A wani labarin, wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun harba bindiga a hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya ta Zone 1 da ke BUK road a Kano, Daily Nigerian ta rahoto.

Ita ma jaridar Leadership ta rahoto cewa wata majiyar tsaro ta ce yan ta'addan sun zo a motocci guda uku misalin ƙarfe 12.30 na ranar Juma'a suka yi harbe-harbe sannan suka tsere.

Majiyar tsaron ta ce an tsaurara tsaro a kusa da hedkwatar yan sandan domin kare afkuwar yiwuwar hari daga yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel