Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

  • Hukumar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce Jirginta ya halaka kasurgumin ɗan ta'adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaka a Kaduna
  • Jirgin ya kuma yi raga-raga da maboyar su da kayan aiki a kauyen Ukambo mai kilomita sama da 100 tsakaninsa da garin Kaduna
  • Mutum 26 da ake zargin yan ta'addan sun yi garkuwa da su sun kubuta sanadin luguden wuta sojin sama

Kaduna - Rundunar Sojojin saman Najeriya (NAF) ta halaka ƙasurgumin shugaban yan ta'adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaƙansa guda 17 a jihar Kaduna, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Alhaji Shanono da yan tawagarsa sun bakunci lahira ne a wurin wani taro a Ukambo, wani ƙauye mai nisan kilomita 131 daga Kaduna lokacin da jirgin rundunar Operation Whirl Punch ya musu luguden wuta ranar Talata.

Jirgin yakin NAF.
Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Kakakin hukumar sojin saman, Edward Gabkwet, ya ce sama da bindigu 30, Babura 20 luguden wuta ya ragargaza yayin da wasu mutum 26 da ke tsare hannun yan ta'addan suka kubuta.

Yadda lamarin ya faru

Channels ta rahoto cewa Wannan na samame na ɗaya daga cikim nasarorin da hukumar doji ta samu a yankin, inda kakakin ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Samamen da jirgin NAF ya kai ya yi sanadin sheƙe yan ta'adda da dama tare da rugurguza maɓoyarsu. Ɗaya daga cikin irin waɗan nan farmakin da Jirgi ya kai jiya 9 ga watan Agusta ya halaka sanannen shugaban yan ta'adda a Kaduna."
"Bayan samun bayanan sirri a jiya cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Alhaji Shanono, ya shirya taro da mayakansa a kauyen Ukambo kilomita 131 daga Kaduna, nan take Jirgin Operation Whirl Punch ya tashi zuwa wurin."

"Da ya isa wurin ya hangi yan ta'addan, bayan sharar fage da gano babu fararen hula kusa, jirgin ya samu izini ya saki ruwan wuta. Bayanai daga yankin sun nuna cewa harin ya lalata bindigu sama da 30 da babura 20."

Majiyar ta ƙara da cewa, "Yan ta'adda 18 cikin su har da Alhaji Shanono sun bakunci lahira, sauran kuma suka jikkata. Kaka kuma aƙalla fararen hula 26 da yan ta'adda ke tsare da su suka kubuta sanadin samamen."

A wani labarin kuma Basarake Ya Haɗa Yan Daba da Muggan Makamai, Sun Kai Farmaki Fadar Sarkin Gargajiya a Arewa

An garkame Basaraken Samora bisa zargin ya haɗa yan daba sun farmaki wani sarkin gargajiya, Oloba na ƙasar Eju a jihar Kwara.

Yayin zaman Kotun na yau, mai gabatar da ƙara ya faɗa wa Kotun cewa maharan sun illata Oloba da iyalansa sun sace masa kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel