Yadda Boko Haram, ISWAP da Ansaru ke haɗin gwiwa da shugabannin ƴan bindigan arewa

Yadda Boko Haram, ISWAP da Ansaru ke haɗin gwiwa da shugabannin ƴan bindigan arewa

  • Rahotanni sun nuna cewa kungiyoyin yan ta'adda na ISWAP, Boko Haram da Ansaru na ta janyo yan bindigan arewacin Nigeria a jika
  • Wasu daga cikin shugabannin yan bindigan irin su Dogo Gide da Turji tuni sun amsa kiran yan ta'addan sun fara aiwatar da tsare-tsare irin nasu
  • Kwararru a fanin tsaro da mazauna yankunan sun tabbatar da wannan hadin gwiwar tare da bayyana hatsarin da ke tattare da hakan

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyoyin ta'addanci na Jama’atu Ahlul Sunnah lid Da’awatu wal Jihad (Boko Haram) da Islamic State in West Africa Province (ISWAP) da Jama’atu Ansarul Muslimina fii Biladis Sudan (da aka fi sani da Ansaru) suna gasar neman mabiya daga cikin 'yan bindiga da ke adabar jihohin arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.

Kwararru a bangaren tsaro da mazauna yankunan da suka yi magana da wakilin Daily Trust sun tabbatar da cewa kungiyoyin ta'addancin tuni sun fara samun nasara a wannan yunkurin inda wasu daga cikin shugabannin yan bindigan sun fara musu mubaya'a ko aiki tare da musayar bayanai.

Babban hafsan sojojin kasa na Nigeria, Faruk Yahaya
Babban hafsan sojojin kasa na Nigeria, Faruk Yahaya. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ɗan majalisar jihar Nigeria ya yanke jiki ya faɗi matacce

Jihohin da matsalar yan bindigan ta fi shafa sune Niger, Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi. Jihohin na da iyakoki kuma an iya shiga da fita tsakaninsu cikin dazuka.

Binciken da majiyar Legit.ng ta yi ya nuna cewa a kalla kungiyoyin uku na rububin neman mambobi daga kungiyoyin yan bindiga da ke kai hare-hare a jihohin na arewa.

Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, bata amsa sakon da aka aike mata ba na neman ta yi tsokaci a kan wannan labarin.

Yunkurin daukan neman sabbin mambobi

Majiyoyi masu nagarta, tunda dadewa sun sanar da Daily Trust cewa tsagin Abubakar Shekau na kungiyar Boko Haram da ISWAP sun yi kokarin kutsawa jihohin arewa maso yammacin Nigeria da Nijar domin amfana daga rudani da hare-haren yan bindiga ya janyo a yankunan da kuma raba kan jami'an tsaro da suka mayar da hankali wurin dakile yan ta'adda a jihohin Borno da Yobe.

Ansaru, wadda aka ce ta fara kafa sansani a Okene, jihar Kogi ta fara hadin gwiwa da yan bindiga karkashin shugabancin Dogo Gide a kusa da dajin Kuyambana a jihar Kaduna.

Wani shugaba na siyasa daga yankin, a cikin 2020, ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa Dogo Gide ya hada kai da Ansaru sun kafa na'urar inganta sadarwa a cikin dajin Birnin Gwari domin saukaka sadarwa tsakaninsa da wasu bata garin daga waje.

Wani majiya da ke da kusanci da Gide, wanda kuma ya nemi a sakayya sunansa ya ce Gide ya shafe kimanin shekaru uku yana aiki tare da Ansaru.

"Mambobin Ansaru sun iso arewa maso yamma tun 2012 amma a baya-bayan nan suna kokarin farfadowa. Daya daga cikin manufofinsu shine janyo miyagun mutane da mazauna yankunan arewa maso yamma cikinsu. Hakan yasa suka fara yin wa'azi da harshen Fulatanci tare da bawa manoman yankunan kananan rance," Bukarti ya shaidawa Daily Trust.

Shugabannin yan bindiga sun fara amfani da dokokin shari'a

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin shugabannin yan bindiga sun karbi wa'azin da yan ta'addan ke musu har sun fara aiwatar da dokoki masu tsauri a tsakanin mutanensu.

Wasu daga cikinsu sun hana abubuwan ki kamar shan abubuwan maye, satar shanu a yankunansu da sauransu.

A hirar tarho da aka yi da shi, Gide, ya yi ta nanatawa cewa yana da makarantar Islamiyya da ya saka daliban da ya sace.

Ya kuma yi barazanar cewa zai mayar da su mayakansa sannan ya aurar da matan cikinsu ga mayakansa a wani abu da ya yi kama da tsarin ISWAP.

A wani yanki tsakanin Zamfara da Kagara a jihar Sokoto, wani dan bindiga mai suna Turji shima ya fara aiwatar da irin wannan tsarin a yayin da mazauna garin ke jita-jitar cewa shima ya fara hada kai da yan ta'addan.

KU KARANTA: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

Wannan hadin kan abu ne mai hatsari, Kwararu

A martaninsa, Bukarti, wanda ya yi nazarin kungiyoyin ta'addanci a yankin Sahel ya ce hadin kai tsakanin kungiyoyin ta'addanci da yan bindiga abu ne mai hatsari da ya zama dole gwamnati ta dauki mataki a kai.

Ya ce:

"Boko Haram na iya bada dalilai da ke hallasta kashe-kashe da harin da suke kaiwa."
"Idan bata gari da ya saba halaka mutane ya fara ganin barnar da ya ke yi jihadi ne ba laifi ba, abin da ya ke aikatawa za ta kazanta.
"Na biyo, hadin kai da Boko Haram zai bawa bata garin damar samun matasa da za su shiga kungiyarsu wanda a baya ba dole ne su shiga ba."

Bukarti na fargabar Boko Haram na iya koyar da yan bindigar hada bama-bamai da wasu abubuwa masu hadari.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel