An Kama Yan Bindiga da Masu Safarar Kwayoyi Sama da 10 a Kaduna Cikin Wata Shida

An Kama Yan Bindiga da Masu Safarar Kwayoyi Sama da 10 a Kaduna Cikin Wata Shida

  • Jami'an rundunar yan Banga wato Yan Bijilanti sun yi nasarar kama mutum 100 da ake zargi da aikata manyan laifuka a Kaduna
  • Kwamandan KADVS, Birgediya Janar Umar Ibrahim mai ritaya, ya ce sun kama yan bindiga, masu garkuwa da masu safarar kwayoyi
  • A cewarsa sun samu wannan nasarar ne cikin watanni shida da suka gabata, kuma ba komai suka faɗa ba

Kaduna - Sama da mutanen da ake zargi 100 ne suka shiga hannun rundunar yan Bijilanti a jihar Kaduna cikin watanni 6 da suka shuɗe bisa zargin aikata laifuka daban-daban.

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa ana zargin mutanen da aikata laifuka da duka haɗa da, ta'addancin yan fashin daji, garkuwa, da safarar miyagun kwayoyi.

Birgediya Umar Ibrahim Mai ritaya.
An Kama Yan Bindiga da Masu Safarar Kwayoyi Sama da 10 a Kaduna Cikin Wata Shida Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a bayanan kwamandan rundunar, Birgediya Janar Umar Ibrahim mai ritaya, lokacin da yake nuna masu safarar miyagun kwayoyi uku da aka cafke a sassan Kaduna.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu, Wani Mutumi Ya Kai Karar Surukansa, Ya Ce Sun Yi Garkuwa da Matarsa Mai Tsohon Ciki

A jawabinsa ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jimulla, mun kama mutum 100 da suka haɗa da yan bindiga zuwa masu safarar kwayoyi. Tabbas muna da ƙarfi, abun da muke bukata kawai kwarin guiwa."
"Gwamnati na iya bakin kokarinta wajen taimaka wa KADVS a yaƙi da ta'addanci tare da sauran hukumomin tsaro, muna yin iya namu, ba wani abu bane da sai mun fito mun faɗa wa duniya abinda muke yi."

Yadda muka ɗamƙe mutanen - Kwamandan KADVS

Da yake damƙa waɗan da ake zargin da kwayoyin ga wakilan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Ibrahim ya ce dakarunsa sun kama su ne biyo bayan bin diddigi kan ayyukan su.

Ya ƙara da bayanin cewa baki ɗaya mutanen da ake zargin sun shiga hannu ne yayin wani Sintiri a sassan ƙananan hukumomin Kaduna 23. A cewarsa akwai alaƙa tsakanin ayyukan yan bindiga da masu harkar kwayoyi.

Kara karanta wannan

Amotekun Ta Kara Kama Matafiya 168 Daga Yankin Arewa Saboda Rashin Hujjar Shiga Jihar Su

Kwamandan ya yi kira ga mazaunan Kaduna su baiwa hukumomin tsaro haɗin kai domin cimma nasara a yaƙin da suke da masu garkuwa, yan bindiga a jihar.

A wani labarin kuma Yan Majalisar dokokin jihar Katsin sun yanke zuwa ganin Masaari da Buhari don tattaunawa kan halin rashin tsaron jihar

Mambobin majalisar dokokin jihar Katsina zasu gana da gwamna Masari da shugaba Buhari kan rashin tsaron jihar.

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne yayin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar, mahaifar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel