Rikicin Rabon Gado: Sarkin Zazzau Ya Dakatar da Dagaci daga Kujerarsa

Rikicin Rabon Gado: Sarkin Zazzau Ya Dakatar da Dagaci daga Kujerarsa

  • Sarkin Zazzau ya umarci hakiman Kudan da Hunkuyi su kula da sake rabon gadon cikin adalci bayan barkewar rigima kan haka
  • Bayan bincike mai zurfi, masarautar ta dakatar da dagacin wani ƙauye tare da kwato kuɗaɗen da aka raba wa waɗanda ba su cancanci gado ba
  • Hakan ya biyo bayan sasanta rikicin rabon gado a Matarawa, tare da gargadin hakimai da dagatai su guji zaluntar marasa ƙarfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Majalisar Masarautar Zazzau ta shiga tsakani a wani rikicin rabon gado da ya taso a Matarawa da ke Gundumar Kudan.

Masarautar ta yi gargadi ga dagatai da sauran masu rike da sarauar gargajiya karkashinta kan zaluntar marasa ƙarfi da ke yankunansu.

Sarkin Zazzau ya dakatar da dagaci
Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli a jihar Kaduna. Hoto: Zazzau Emirates.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar wanda masarautar ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Babu imani: Wani ɗan masu kuɗi ya caccaka wa mahaifinsa wuka har lahira a Abuja

Dagaci ya rasa kujerarsa kan rikicin gado

Sanarwar ta ce an yanke hukuncin ne bayan zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Sarkin Zazzau.

A bayaninsa, Kwarbai ya ce an kawo ƙorafin sau uku gaban majalisar, inda aka yi zargin wasu magada na gaskiya ba su samu haƙƙinsu ba.

Haka kuma, an bayyana cewa wasu mutanen da ba su cancanci gadon ba sun amfana da rabon dukiyar marigayin ba bisa ƙa’ida ba.

Bayan gudanar da bincike mai zurfi, majalisar ta dakatar da dagacin ƙauyen da abin ya shafa tare da umartar dawo da kuɗaɗen da aka raba ba bisa ka’ida ba.

An kuma tattara kuɗaɗen da aka dawo da su tare da miƙa su ga Sarkin Zazzau domin tabbatar da sake rabonsu cikin gaskiya da adalci.

Sarkin Zazzau ya yi gargadi kan zalunci
Taswirar jihar Kaduna da Masarautar Zazzau ke karkashinta. Hoto: Legit.
Source: Original

Umarnin da Sarkin Zazzau ya bayar a yankinsa

Daga bisani Sarkin Zazzau ya ba hakiman Kudan da Hunkuyi umarnin komawa Matarawa domin kula da yadda za a sake rabon gadon bisa dokokin Musulunci.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Sanarwar ta ƙara da cewa Sarkin ya ja kunnen hakimai da dagatai su kula da yadda jami’ansu ke mu’amala da talakawa a masarautar.

Sarkin ya ce masarautar ba za ta lamunci duk wani nau’in yaudara ko cin zarafin marasa ƙarfi daga masu mulki ko jami’ansu ba.

Ya kuma jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana ga shugabannin gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya da adalci tsakanin al’umma.

Majalisar Masarautar Zazzau ta ce za ta ci gaba da amfani da sulhu da sasanci wajen warware rikice-rikice da kare talakawa daga danniya.

An dakatar da dagaci, kansila a Gombe

Kun ji labarin cewa Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta dauki mataki kan kansila da dagaci bisa zargin sata.

An zargi kansilan da dagacin da hada baki wajen sace randar wutar lantarki a Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko da ke jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya sanar da haka a yau Jumu'a, 28 da watan Yunin shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.