Latest
Jam'iyyar PDP ta daura alhakin harin da aka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kano kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Labarin da muke samu ya bayyana cewa, an kama wasu mutane da ake zargin suna siyar da sabbin Naira ga mazauna a babban birnin tarayya Abuja a cikin makon nan.
An samu barkewar rikici a tsakanin mazauna Kano da jami’an tsaro bayan ziyarar aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar a ran Litinin, 30 ga watan Janairu.
A ranar Litinin ne kotun Koli ta tabbatar da Sanata Adamu Aliero a matsayin 'dan takarar kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Geamnan jihar Ribas kuma jagoran gwamnonin G5, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Ayu ya ɗebo ruwan dafa kansa tunda har ya umarci lauyoyin PDP su janye a Ribas.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya sake yin wata katobarar da ta tafi ta baya, ya ce Atiku Abubakar ya kasance shugaban majalisar dattawa na Najeriya.
Wani mutum ya haddasa yar dirama a asibiti yayin da wata malamar jinya ta yi yunkurin karbar samfurin jininsa don gwaji; ya tsorata da allura inda ya yi ta ihu.
Wani matashi ya tsinci kansa a wata kasa a daidai lokacin da yake tsaka da wasa da wasu abokansa. Rahoto ya bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru da matashi.
A jihar Ribas abin bai yi kyau ba, domin ‘Yan daba sun je kauyen ‘dan takaran majalisa, sun kona masa gida. Ezemonye Ezekiel-Amadi ya shaida haka a wani bidiyo.
Masu zafi
Samu kari