Ziyarar Shugaba Buhari Jihar Kano Ya Bar Baya da Kura, Rikici Ya Barke

Ziyarar Shugaba Buhari Jihar Kano Ya Bar Baya da Kura, Rikici Ya Barke

  • A yau Litinin, 30 ga watan Janairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kano inda ya kaddamar da wasu ayyuka
  • Bayan ziyarar da Buhari ya kai jihar ta arewa, wasu fusatattun matasa sun fito sun yi zanga-zanga tare da yi masa ihun 'ba ma yi'
  • Lamarin baya rasa nasaba halin wayyo Allah da talakawa suka shiga sakamakon sauya takardun naira da tsadar man fetur a kasar

Kano - Fusatattun mazauna jihar Kano sun fito don yin zanga-zanga kan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar don kaddamar da wasu ayyukan gwamnati a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa rikici ya barke tsakanin al'ummar jihar Kano da jami'an tsaro jim kadan bayan Buhari ya bude gadar sama a unguwar Hotoro.=

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ganduje ya Bayyanawa Buhari Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

Wurin zanga-zanga
Ziyarar Shugaba Buhari Jihar Kano Ya Bar Baya da Kura, Rikici Ya Barke Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Wani da abun ya faru kan idanunsa ya sanar da jaridar cewa jami'an yan sanda sun yi ta harbi amma dai bai samu kowa ba inda mutane suka dunga ihu da jifan ma'aikatan tsaron.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A yanzu haka yan sanda na ta harbi amma ba a harbi kowa ba; su ma jama'a suna ta ihu da jifan ma'aikatan."

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa fusatattun matasan sun kunna wuta a hanyar Maiduguri Road da ke birnin jihar sannan suka dungi ihun 'ba ma yi' tare da jifan ayarin motocin da duwatsu daga nesa duk da tsaurara tsaron da aka yi tare da harba barkonon tsohuwa.

An kuma tattaro cewa zanga-zangar baya rasa nasaba da mawuyacin halin da yan Najeriya ke fuskanta sakamakon hauhawan farashin man fetur da kuma karancin sabbin kudade da aka sauya.

Kara karanta wannan

Akwai Babban Tanadi Da Na Yi Wa Yan Arewa Idan Na Zama Shugaban Kasa, Obi

A bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an gano wasu matasa suna ta jifan jirgin shugaban kasar yayin da ya tashi bayan kaddamar da aikin sola a Zawaciki.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan irin haka ya faru a mahaifar shugaban kasar wato jihar Katsina.

Ganduje ya nemi Buhari ya dakatar da zuwansa jihar Kano

Tun farko dai Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci shugaban kasar da ya dakatar da zuwansa jihar saboda halin da talakawa ke ciki sakamakon sauya kudaden kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel