A Sabon Batu, Tinubu Ya Sake Tafka Katobara a Zancensa a Jihar Akwa Ibom

A Sabon Batu, Tinubu Ya Sake Tafka Katobara a Zancensa a Jihar Akwa Ibom

  • A wani sabon zubin, dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya sake yin wata katobara
  • Tinubu ya ce Atiku ne tsohon shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, kuma ya siyar da kadarori da yawa
  • Ba wannan ne karon farko da Tinubu ke samun cakudewar tunani ba, ya sha yin hakan a baya

Uyo, jihar Akwa Ibom – Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a APC ya sake yin wata katobarar da ta tafi ta baya gabanin zaben 2023.

Ya tafka katobara a magana inda ya kalli mabiya bayansa a jam’iyyar APC ya a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Litinin 30 ga watan Fabrairu ya yi musu magana game da Atiku.

A wannan karon, Tinubu ya ce, dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya kasance shugaban majalisar dattawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya anar da Muhimmin Taimakon da Yayi wa Atiku Yayin Rikicinsu da Obasanjo

Tinubu ya kwafsa a jihar Akwa Ibom
A Sabon Batu, Tinubu Ya Sake Tafka Katobara a Zancensa a Jihar Akwa Ibom | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A zahirin gaskiya, Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya daga 1999 zuwa 2007 bai taba rike mukamin shugaban majalisar dattawa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani bidiyon da aka yada a Twitter, an ji Tinubu ya cewa:

“Atiku, lokacin da muka daura shi shugaban sanatoci...haba...ka siyar da wannan, ka siyar da wancan. Kadarorinmu, arzikinmu, gadonmu. Komai da muke dashi, ka siyar dashi.”

Martanin jama'a

Bayan ganin bidiyon, mutane da yawa a kafar sada zumunta sun shiga mamaki tare da yin martani. Ga kadan daga ciki:

@kenstine:

"Meye yasa ba za ku bar Tinubu ya tafi neman magani ba! Bai gane mutanen da ke kusa dashi."

@Iyanumashele10:

"Sanata atiku ."

@CyrusAdemola:

"Wannan jam'iyyar barkwanci ce."

@Whiz_Rahman:

"Bayan kiransa gwamnan Anambra, yanzu kuma shugaban sanatoci...Kai wa muka sabawa ne a kasar nan ne ."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano

@Mrjusticenwosu:

"Wannan batu ne mai girgizarwa daga mai girma Jagaban, Jagaban ya kasance a cikin daura mutane kan turba."

Tinubu ya kwafsa a lokacin da yake magana a filin kamfen

A wani labarin, kunji yadda aka ruwaito Tinubu ya kwafsa a wani taron kamfen na APC da ya halarta a daya daga jihohin Najeriya.

Tinubu ya yi kuren harshe, inda yace ya tanadarwa 'yan Najeriya tsadar abinci da kayayyaki idan ya gaji Buhari.

Dama ana ci gaba da zargin Tinubu bai da cikakkiyar lafiya, batutuwansa na ci gaba da nuna alamun haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel