Nakiya Ta Yi Kaca-Kaca da Masallaci, Makaranta da Gida a Jihar Bauchi

Nakiya Ta Yi Kaca-Kaca da Masallaci, Makaranta da Gida a Jihar Bauchi

  • Wani abu da ake zaton nakiya ce ya fashe a garin Azare, karamar hukumar Katagum, jihar Bauchi
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Aminu Alhassan, yave babu wanda fashewar ta kashe amma Masallaci, makaranta da gida sun lalace
  • Gwamna Bala Muhammed ya bukaci mazauna jihar da su baiwa jami'an tsaro haɗin kai wajen bincike

Katsina - Wani abun fashewa da ake kyautata zaton Nakiya ce ta lalata gida, Masallaci da Makaranta a garin Azare, hedkwatar ƙaramar hukumar Katagun a jihar Bauchi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Aminu Alhassan ne ya bayyana haka ranar Litinin a fadar mai martaba Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk II da fadar Galadiman Katagum, Alhaji Usman Mahmood Abdullahi.

Taswirar jahar Bauchi.
Nakiya Ta Yi Kaca-Kaca da Masallaci, Makaranta da Gida a Jihar Bauchi Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kwamishinan ya ziyarci fadar Sarakunan ne domin raka gwamna Bala Muhammed su jajantawa mutanen da fashewar ta shafa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Ruɗani, Manyan Jiga-Jigan PDP Da Dubannin Mambobi Sun Koma APC a Arewa

Yace fashewar ta faru ne sakamakon akasin da aka samu babu wanda ya mutu amma gine-gine sun lalace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa an samu fashewar abun ne bayan mutane sun tara ciyayin wurin guri ɗaya sannan suka cinna masu wuta.

Ya ce:

"Muna zargin wani abun fashewa kamar Nakiya aka binne a yankin tun shakaru sama da 30 da suka shuɗe saboda wani kamfanin gina Tituna ya taba zama a wurin."
"Akwai wani lokaci can a baya da Boko Haram ta kai hari Caji Ofis ɗin Azare, ta hanyar da abun ya tashi mayaƙan kungiyar ta'addancin suka biyo, har yanzu muna ta bincike."

CP Aminu Alhassan ya kara da cewa tuni tawagar sashin kwance Bam suka mamaye wurin domin binciko ainihin abinda ya haddasa tashin nakiyar.

Bugu da ƙari, Kwamshinan ya bayyana cewa zuwa yanzun sun gano abubuwan fashewar da aka ɗana guda biyu a yankin, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Sight and Sounds' Ta Shirya Taro Kan Manufofin Asiwaju Bola Tinubu

Gwamnati zata biya diyya - Kauran Bauchi

A nasa jawabin, gwamna Bala Muhammed ya sha alwashin biyan diyya ga wadanda abun ya shafa kana ya miƙa godiya ga Allah da ya tsare ba wanda ya rasa rai.

Ya roki mutanen da abun ya shafa su ɗauka kaddara ce daga Allah kana ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Ya kuma roki mazauna yankin su baiwa jami'an tsaro haɗin kai ko da kuwa sun nemi sauya masu wurin zama domin su kakkaɓe duk wani abun fashewa dake wajen, ya basu tabbacin gwamnati zata tallafa masu.

A wani labarin kuma Gwamnan Sule Ya Fallasa Wanda Ya Kai Harin Bam Kan Makiyaya a Nasarawa

Akalla Makiyaya 27 aka tabbatar sun mutu a wani tashin Bam da ya auku a garin Kwateri mai iyaka tsakanin Nasarawa da Benuwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel